Siyasar Kaduna yanzu bata ubangida bace, inji El-Rufai

Siyasar Kaduna yanzu bata ubangida bace, inji El-Rufai

-Ni na kori siyasar ubangida a jihar Kaduna, a cewar El-Rufai

-Legas ma zata iya kau da wannan abu na siyasar ubangida, sai dai yin hakan yanada bukatar lokaci da kuma kyakkyawan shiri, inji Mallam Nasiru El-Rufai

Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai na jihar Kaduna a ranar Assabar ya fadi cewa yasan yadda za’a kawo karshen siyasar ubangida a jihar Legas. Gwamnan yayi wannan furucin ne wurin wani taro da ya gudana a Bridge club dake Ikoyin jihar Legas.

Nine na kawo karshen siyarsar ubangida a Kaduna, za’a iya yin hakan ma a Legas, inji El-Rufai
Gwamna El-Rufai
Asali: UGC

KU KARANTA:Ganduje zai sauke dukkanin 'yan Majalisar gwamnatin sa, zai nada wadanda ba ya da shakkun biyayyar su a gare sa

Yace: “ Siyasar ubangida, nan fa Legas ce; bari in fada maka wani abu yallabai, a baya muna da mutum uku zuwa hudu a Kaduna wadanda baka iya zamowa wani a jihar face kana tare dasu."

“ Wadannan sune masu juya akalar siyasar Kaduna, duk abinda zakayi sai ka hado dasu. Abinda nake nufi shawararsu itace abin bi duk yadda su kace ayi hakan za’ayi.

“ A zaben 2019, sai muka sauya salo inda muka samu nasarar yi masu ritaya a jihar Kaduna gaba dayansu.”

Zance akan yadda za’a kau da siyasar ubangida a Legas kuwa, gwamnan yace babban abinyi shine samun mutane tun daga tushensu.

Legas ta kasance karkashin Bola Tinubu tun lokacin da ya kasance gwamnan jihar a karo na farko. Ya cigaba da samun katabus inda ake damawa dashi a siyasar Legas kai kama iya cewa shine yake da alhakin tsayar da gwamnoni uku da suka biyo bayansa cikin hadda zababben gwamnan Legas Babajide Sanwoolu.

Kafin ya kasance an taka masa birki, akwai bukatar mutum ya tsaya ya fahimci siyasar Legas wacce ke da kusan kuri’u miliyan biyar zuwa shida amma ba gaba dayansu sukai zabe ba.

“ Zan baku shawarar neman wadannan mutane miliyan biyar ko shida tareda jin dalilinsu na rashin yin zabe. Akwai na’urar tantance kati zabe wacce ta saukaka mana komi. Sai dai abu ne mai matukar wahala kwarai dagaske. Domin cin manufar zabe mai zuwa tun yanzu yakamata a fara yinsa da kadan kadan.” Inji El-Rufai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel