Yadda tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon ya fadi a cikin Makabarta

Yadda tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon ya fadi a cikin Makabarta

- Tsohon shugaban kasar Najeriya a lokacin mulkin soja, Janar Yakubu Gowon, ya yanke jiki ya fadi yayin halartar wata Jana'iza a jihar Delta

- Gowon ya fadi a gabar Kabarin Marigayi Manjo Janar David Akpodite Ejoor yayin jana'izar sa a yankin Ovwor-Olomu na karamar hukumar Ughelli ta Kudu

Sabon rahoto ya bayyana dangane da yadda tsohon shugaban kasa a lokacin mulkin soja, Janar Yakubu Gowon, ya yanke jiki ya fadi ana tsaka da jana'izar Marigayi Manjo Janar David Akpodiete Ejoor a yankin Ovwor-Olomu na jihar Delta.

Yadda tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon ya fadi a cikin Makabarta

Yadda tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon ya fadi a cikin Makabarta
Source: Depositphotos

Tsohon shugaban kasa Gowon ya yanke jiki a gabar kabarin Marigayi Manjo Janar David Akpodiete Ejoor bayan tsayuwa ta tsawon awanni da dama.

Rahotanni kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito sun bayyana cewa, tsohon shugaban kasa ya nemi aminin sa kuma tsohon karamin ministan ilimi, Olorogun Kenneth Gbagi, da ya janye shi daga gabar kabarin tun gabanin ya yanke jiki.

KARANTA KUMA: 'Yan siyasa 15 na jihar Kuros Riba na neman kujerar Minista a Majalisar Buhari

Wani babban jami'in tsaro ya bayyana cewa, gajiya bayan tsayuwa ta tsawon awanni ta sanya tsohon shugaban kasa ya yanke jiki ya fadi ana tsaka da jana'izar tsohon shugaban hafsin sojin kasa, a karamar hukumar Ugehelli ta Kudu a jihar Delta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel