Wani mutum ya mutu ana daf da daura masa aure

Wani mutum ya mutu ana daf da daura masa aure

-Ana bikin duniya ake na lahira, wani mutum ya mutu yana daf da angwancewa

-Matashin ya mutu yan awanni kadan kafi a daura mashi aure, sai dai ba'a gano dalilin mutuwarsa ba har yanzu

Labari yazowa majiyar Legit.ng cewa wani mutum mai suna Yahaya Abdul da ya fito daga jihar Kogi yayi mutuwar ban mamaki.

Mamacin wanda ke aikin kanikanci yana daf da angwancewa a ranar 4 ga watan Mayu yayinda da aka samu labarin mutuwarsa a gidansu.

Wani mutum ya mutu ana daf da daura masa aure

Wani mutum ya mutu ana daf da daura masa aure
Source: Facebook

KU KARANTA:Sabon shugaban NYSC ya shiga ofis

Rahotanni sun tabbatar da cewa iyalansa na cikin juyayi da bakin cikin wannan abu da ya auku, dalilin da ya sanya aka dakatar da duk wasu shirye shirye da ake na bikin.

A halin yanzu dai ba’a san dalilin mutuwarsa ba, amma sai dai ya samu shaidar cewa mutum ne da baida kyuyar aiki kuma sananne a unguwar Omeda dake jihar Kogi inda shi mamacin yake da zama.

Dan uwansa Baba Hassan Yusuf shine ya sanar da wannan labarin a shafinsa na facebook inda ya sanya hotunan marigayin tare da amaryasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel