Za a fara Sallatar Juma’a a Masallaci mafi girma dake kasar Turkiyya

Za a fara Sallatar Juma’a a Masallaci mafi girma dake kasar Turkiyya

A ranar yau Juma'ar, 3 ga watan Mayu ne za a fara gudanar da Ibada a Masallacin Juma'a na Camlica dake birnin Istanbul a Turkiyya wanda shine mafi girma a kasar. An tattaro cewa an fara gina Masallacin ne tun shekaru shida da suka gabata.

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan zai halarci bukin bude Masallacin da za a yi bayan an yi Sallar Juma'a.

Akwai manyan mutane daga ciki da wajen Turkiyya da aka gayyata zuwa bude Masallacin.

Za kuma a ci gaba da karanta Alkur'ani Mai Tsarki har zuwa daren wannan rana ta Juma'a.

Za a fara Sallatar Juma’a a Masallaci mafi girma dake kasar Turkiyya
Za a fara Sallatar Juma’a a Masallaci mafi girma dake kasar Turkiyya
Asali: UGC

Masallacin da yake da siffa ta daulolin Usmaniyya da Selcuk zai zama daya daga cikin muhimman alamomin Istanbul.

Sakamakon kyakkyawan ginin masallacin ana iya hango shi daga sassan Istanbul daban-daban.

KU KARANTA KUMA: Kungiyoyin Musulunci sun jinjina wa gwamnatin tarayya kan sakin Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, a yau Juma’a, 3 ga watan Mayu ne za a kaddamar da babban masalacin Juma’a na garin Lafia, babbar birnin jihar Nasarawa wanda aka gyara.

Gwamnan jihar, Alhaji Umaru Tanko Almakura ne ya sanar da hakan lokacin da ya karbi bakuncin babban mamba a masarautar Lafia, Madakin Lafia, Alhaji Ishaku Dauda a yayin rangajin duba matakin da aikin ya kai kafin bikin bude shi.

An gyara masallacin ne domin ya dauki masu bauta da dama sannan kuma a kawata shi da kayayyakin zamani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel