‘Yan sanda sun kama mutum biyu da gawarwaki a jihar Taraba

‘Yan sanda sun kama mutum biyu da gawarwaki a jihar Taraba

-An kama wasu mutum biyu da gawarwaki a karamar hukumar Takum ta jihar Taraba

-Shugaban karamar hukumar Takum yace mutanen da aka kama yan sintirine ba wai yan ta'adda ba

Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta samu nasarar damke wasu mutane biyu daidai lokacin da suke kokarin jefar da gawarwaki guda biyu a shiyyar Kwambai dake karamar hukumar Takum.

Da yake magana da yan jarida jami’in hulda da jama’a na yan sandan jihar, DSP David Misal yace kwamishinan yan sanda ya bada umurnin cewa mutanen da aka kama cikin motar Toyota kirar Hilux da akawosu Jalingo domin tuhumarsu.

‘Yan sanda sun kama mutum biyu da gawarwaki a jihar Taraba

‘Yan sanda sun kama mutum biyu da gawarwaki a jihar Taraba
Source: UGC

KU KARANTA:Buhari ya sauyawa ma’aikantasa wurin aiki kafin a rantsar dashi a karo na biyu

Yace duk da cewa har yanzu babu gamsasshen bayani akan yadda lamarin ya auku, an tura da wadannan mutane zuwa shelkwatar yan sanda ta Jalingo domin a bincikesu akan yadda suka samo gawarwakin.

Ana shi bayanin, shugaban karamar hukumar Takum yace, gawarwakin wasu yan fashine da yan sintiri suka kashe, kuma an kamasu ne yayinda suka sanya gawarwakin cikin Hilux domin jefar dasu.

Yan sintirin dai sun kasance suna taimakawa yankin nasu ta wurin yaki da ‘yan bindiga da kuma yan fashi wadanda suka dade suna addabar yankin.

Shiban Tikari yace abin yayi matukar bashi mamaki ganin labaran dake yawo a shafukan sadarwa. Sam wannan batu bah aka yake ba, mutanen da basu son ganin mun zauna lafiyane suke yada wannan labarin sabanin garkiyar lamarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel