Wata mata ta kai mijin ta kotu sanadiyyar marin ta a gaban ‘ya’yanta

Wata mata ta kai mijin ta kotu sanadiyyar marin ta a gaban ‘ya’yanta

Wata mata ta kai mijin ta kotu sanadiyyar m a g

Wata matar aure ‘yar shekaru 25, mai suna Maryam Abdullahi ta kai mijinta kara a Kotun Shari’a mai daraja ta II, dake Magajin Gari a jihar Kaduna, sanadiyyar marin ta a gaban ‘ya’yansu.

Maryam, wadda ke zaune a Hayin Malam Bello, jihar Kaduna, tayi zargin cewa mijinta ya mare ta saboda wata ‘yar rashin fahimtar da ta shiga tsakanin su.

“Na tafi gida don ganin mahaifana, wadanda gidansu ba ya da nisa da inda muke zaune. A lokacin da na dawo, bai saurari dalilin da ya sa na je ganin su ba.

Maryam tace: ”Ya mare ni a kuncina na dama kuma ya kumbure,”

Wanda ake kara Ismail Abdullahi, mai shekaru 45, wanda ke sana’ar gini ya yarda da cewa ya mari matarsa.

“Kullum tana zuwa yawo ta bar yara a gida ba tare da izini na ba. Ina rokon kotu ta tausaya man, ba zan sake dukan ta ba. Ina son matata.” In ji Isama’il.

Baban wadda ke kara, Malam Muhammad Lawal, ya roki kotu da ta tsawata ma wanda ake kara da ya bar dukan ‘yarsa.

Alkalin dake shari’a, Musa Sa’ad-Goma, ya umurci wanda ake kara da ya roki matarsa ta yafe masa a gaban kotu.

Mai shari’a Sa’ad-Goma ya gargade shi da kar ya sake duka ko marin matarsa, ko wane irin sabani ne suka samu.

Alkalin kuma ya umurci wanda ake kara da ya rubuta takardar alkawari wadda dan’uwansa zai kasance shaida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel