Madalla: An yi wa makafi rabon manhajar karatun Alkur'ani

Madalla: An yi wa makafi rabon manhajar karatun Alkur'ani

Rahotanni sun kawo cewa daga cikin kokarin da ake na saukaka wa makafai hanyar karatu da haddan Al-Kur’ani, an rarrabawa masu littafi mai tsarki na musamman.

Wata kungiyar bayar da agaji ta kasar Qatar ce ta yi rabon Alkur'anin wanda aka yi shi don makafi da masu matsalar makanta.

Daruruwan makafi mata da maza ne daga jihohin daban-daban na Najeriya ne suka samu karbar Alkur'anin, a lokacin bikin rarraba shi da aka yi a babbar birnin tarayya, Abuja.

Kur'anin na makafi dai zai ba su damar koyon karatu da sauraron karatun Alkur'ani da kuma tafsiri a cikin harsunan Turanci da faransanci da kuma larabci.

Madalla: An yi wa makafi rabon manhajar karatun Alkur'ani
Madalla: An yi wa makafi rabon manhajar karatun Alkur'ani
Asali: UGC

Daliban da suka samu kyautar Kur'anin sun fito ne daga jihohin Nasarawa da Niger da Filato da Katsina da kuma birnin tarayyar Najeriya wato Abuja.

Hamdu Muhammad Abdu shi ne shugaban kungiyar agaji ta kasar Qatar ya ce an raba wannan kur'ani na zamani ga makafi domin ba su damar zabin sura ko tafsiri a harsunan Ingilishi da Faransanci da Larabci.

Madalla: An yi wa makafi rabon manhajar karatun Alkur'ani
Manhajar da zai saukaka karatun Alkur'anin ga Makafai
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: An harbi sufeto yayinda yan sanda ke musayar wuta da wadanda suka sace surukin Buhari

Ya ce nan gaba za su kuma ziyarci Sokoto da Borno da kuma Kano

Daliban da suka samu gajiyar wannan Kur'anin sun bayyana cewa zai taimaka masu wajen hadda da tilawa ba kamar a baya ba da dole sai an samu mai karantar da su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel