Gwamnatin tarayya zata tabbatar masu karamin karfi sun samu kulawa akan lafiyarsu

Gwamnatin tarayya zata tabbatar masu karamin karfi sun samu kulawa akan lafiyarsu

- Kula da lafiya abune mai matukar muhimmanci don hakane ma yasa gwamnatin Najeriya bata son barin kowa a baya

- Masu karamin karfi zasu samu kulawar da ta dace fannin lafiya, inji mimistan lafiya

Kowace kasa na da wannan nauyin a kanta na tabbatar da cewa yan kasarta kulawar da ta dace a sashen lafiya. Kulawa da lafiya abu ne wanda duk talakawa da masu karamin karfi mazauna karkara keda bukata da wurin gwamnatin, inji ministan lafiya, Farfesa Isaac Adewole.

Bugu da kari, ministan yace ababen kula da lafiya wadanda ake da bukatarsu a kauyuka ba kowane wurin suka samu kaiwa ba. Wannan dalilin ne ya haifar da matsalolin daake fama dasu lokacin tun daga awon ciki har zuwa haihuwa.

Gwamnatin tarayya zata tabbatar masu karamin karfi sun samu kulawa akan lafiyarsu
Gwamnatin tarayya zata tabbatar masu karamin karfi sun samu kulawa akan lafiyarsu
Source: Facebook

KU KARANTA:‘Yan bingida sunyi awon gaba da mataimakin rajistaran jami’ar jihar Taraba

Ministan yayi wannan jawabin ne yayin wata ganawa da Community Health Influencers Promoters (CHIPS) ranar Talata a Abuja. Inda yayi karin haske da cewa, manufarmu itace samar da kyakkyawan yanayin kula da lafiya na bai daya ta hanyar amfani da kananan asibitocin da muke dasu a karkara.

A cewarsa, “ Wannan shirin na CHIPS an fara shine domin bunkasa asibitocinmu na karkara tare da ma’aikatansu wanda gwamnatin tarayya ta habbaka a shekarun da suka gabata. Manufar a nan shine a samu hadin gwiwa tsakanin masu yin hidima fannin lafiya ya zama suna aiki wuri daya.

“ Jami’an CHIPS zasu rinka ta’allaka aikinsu ne akan mata da kananan yara. Sai kuma binciko bukatun asibitocin domin mu samu damar ciyo bakin wannan matsalar daga bangarenmu. Jami’an har ila yau zasu domin samar da mangunguna da kuma shawarawarin akan cutuka kamar tari, gudawa da kuma zazzabin kananan yara.” Ya fadi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel