Muna da kudirin takara a zaben 2023 - Ali Nuhu

Muna da kudirin takara a zaben 2023 - Ali Nuhu

Shahararren jarumin nan na Kannywood wanda aka fi sani da Sarki, Ali Nuhu ya bayyana cewa wasu daga cikin manyan jariman masana’antar na da niyan tsayawa takara a zaben 2023.

Ali ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da shafin BBC, sai dai jarumin ya bayyana cewa wasu daga cikin su sun taba takara a baya.

"A gaba ma yanzu, yana daga cikin irin kudurin da muke da shi, wasu daga cikinmu su fito a 2023 su tsaya takara," cewar jarumin.

Jarumin ya kara da cewa jarumai irinsu Abba El-Mustapha da Nura Hussaini duk sun taba tsayawa takara a zabukan Najeriya.

Muna da kudirin takara a zaben 2023 - Ali Nuhu

Muna da kudirin takara a zaben 2023 - Ali Nuhu
Source: Depositphotos

Da aka tambaye shi ko su wane ne suke da burin shiga harkokin siyasa ka'in da na'in, sai ya ce: "Ba zan iya fadar suna ba yanzu, saboda abu ne da ke kan matakin shirye-shirye".

An tambaye shi cikin raha ko wata rana za a ga fasta dauke da hoton Ali Nuhu yana takarar shugaban kasa, sai ya kyalkyale da dariya yana cewa: "Ah haba! Gaba daya?"

Daga bisani ya ce "Allah dai ya tabbatar mana da alheri amma dai gaskiya muna da wadannan shirye-shirye."

An kara matsawa da tambayar ko jarumin shi da kansa yana da sha'awar tsayawa takara a zaben Najeriya? Tauraron ya ce "A gaskiya a yanzu ba ni da sha'awa".

KU KARANTA KUMA: Hare-haren Zamfara, Katsina da Kaduna: Ba zamu kyale duk wanda aka samu da hannu ba duk matsayinsa - Buhari

Ali Nuhu ya ce ko da yake shi ba shi da sha'awar yin siyasar takara a yanzu, amma a shirye yake ya mara baya ga duk wani tauraron fim da zai tsaya takara.

An tambaye shi ko idan lokacin da ya yi sha'awar tsayawa takara, shin zai iya janye wa Adam Zango idan takara ta hada su kan wata kujera daya? Ali Nuhu ya ce: "Kwarai kuwa".

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel