Hare-haren Zamfara, Katsina da Kaduna: Ba zamu kyale duk wanda aka samu da hannu ba duk matsayinsa - Buhari

Hare-haren Zamfara, Katsina da Kaduna: Ba zamu kyale duk wanda aka samu da hannu ba duk matsayinsa - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa gwamnatin tarayya ba zata kyale duk mutumin da aka samu da hannu a halaka rayuka da dukiyoyin jama’a a jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna ba.

Buhari wanda yayi Allah wadai da aikin yan fashi a jihohin uku, ya ba shugabannin tsaro umurnin yin duk abunda ya kamata cikin dan kankanin lokaci domin tsige aikin ta’addanci a yankunan jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna.

Shugaban kasar yayi Magana ta bakin Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, wanda ya samu rakiyar shugabannin tsaro na jihar, zuwa ziyarar kauyukan Yar Santa da Tsamiyar Jino a karamar hukumar Kankara domin yiwa mutanen yankin jajen hare-haren ta’addanci da aka kai garuruwan wanda yayi sanadiyar rasa rayuka da dukiyoyin miliyoyin naira.

Hare-haren Zamfara, Katsina da Kaduna: Ba zamu kyale duk wanda aka samu da hannu ba duk matsayinsa - Buhari

Hare-haren Zamfara, Katsina da Kaduna: Ba zamu kyale duk wanda aka samu da hannu ba duk matsayinsa - Buhari
Source: UGC

A cewar wata sanarwa daga mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Abdu Labaran Malumfashi, Masari yace lamarin ba abun yarda bane, inda ya bayar da tabbacin shirin da gwamnati keyi domin magance hakan.

KU KARANTA KUMA: Rikicin Gombe: Shugaba Buhari ya nuna matukar alhini da takaici

Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa, lamarin tsaro abune da ya shafi kowa, kuma cewa babu isassun jami’an tsaro da za a tura dukkanin yankunan kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel