Jana’iza ta rikide zuwa rikici a Gombe

Jana’iza ta rikide zuwa rikici a Gombe

-Ana kukan targade, jana'iza ta juya zuwa rikici a Gombe

-Wasu matasa sun hana a gudanar da jana'iza lami lafiya a Gombe

Yayinda da ake kan gudanar da jana’izar yaran kungiyar boys brigade da aka kashe ranar Litinin din ta gabata a Gombe sai abin kuma ya koma rikici.

Jana’izar dai an farata salun alun inda kuma rikici ya barke daga baya a daidai lokacin da wani gungun matasa suka farma wadanda ke hanyar zuwa jana’izar.

Jana’iza ta rikide zuwa rikici a Gombe
Jana’iza ta rikide zuwa rikici a Gombe
Asali: UGC

KARANTA WANNAN:Jagorancin majalisa ta 9: PDP na shirya kaidin zaben Goje da Ekweremadu

A nan ne kuwa matasa da suka halarci wannan jana’iza suka fito a fusace inda suka fara tsare masu ababen hawa domin ci masu zarafi. A tunaninsu da sa hannun su akeyi masu wannan cin kashin.

Bugu da kari, rikicin dai ya barke ne a daidai titin FCE Gombe.

Wakilinmu ya shaida mana cewa mutane sun kadu kwarai da gaske, inda suke rokon jami’an tsaro da su shiga cikin wannan lamarin domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel