Tinubu ba zai mulki Najeriya ba, inji shugaban Miyetti Allah

Tinubu ba zai mulki Najeriya ba, inji shugaban Miyetti Allah

-Tinubu ba shi ba mulkin Najeriya, ko bayan Buhari ya gama dan arewa ne zai sake hawa

Shugaban kungiyar Miyetti Allah na kasa Abdullahi Bodejo yayi watsi da duk wata magana mai cewa tsohon gwamnan Legas Asiwaju Bola Tinubu shine zai karbi ragamar mulkin Najeriya daga hannun shugaba Buhari a 2023.

Bodejo yayi wannan furucin ne yayin da yake zantawa da jaridar The Sun, ga kuma yadda tattaunawar ta kasance.

Tinubu ba zai mulki Najeriya ba, inji shugaban Miyetti Allah
Tinubu ba zai mulki Najeriya ba, inji shugaban Miyetti Allah
Asali: UGC

KU KARANTA:Jagorancin majalisar dattawa: ‘Yan najeriya zasu samu kyakkyawan jagoranci daga wurina, inji Lawan

Bayan kammala zaben 2019 kashe-kashe ya sake barkewa a arewacin Najeriya, ko menene matsalar?

Na gode ma Allah babu wanda ke dangata kashe-kashen zuwa ga Fulani makiyaya ba kamar a wancan lokacin ba. Zan iya tunawa a shekarar 2014, ina daya daga cikin kwamitin da babban Sufeton ‘yan sanda na wancan lokaci M.D Abubakar ya nada, inda muka zagaya zuwa jihohin Zamfara, Nasarawa, Filato da Taraba.

A wancan lokaci mun samu matsaloli daban-daban tsakanin Fulani da wasu kabilu dake jihohin. Amma abinda ke faruwa yanzu baida alaka da makiyaya kawai dai wasu ‘yna bindiga ke addabar Zamfara da irin nasu ta’addancin.

Me zakace game da zargin da akeyiwa Buhari na nuna halin ko in kula akan kashe-kashen tun baya da yayi nasarar lashe zabe a karo na biyu?

Mutane zasu iya fadin abubuwa daban-daban. Idan Buhari bai damu da abinda ke faruwa mai zai sa shi ya tura sojoji wadannan wurare domin su kawo karshen kashe-kashe? Kawai ni nafi daura laifin wannan surutu akan wanda suka fadi zabe don haka suke fadin duk maganar da tazo bakinsu. Amma ko shakka babu shugaban kasa yana iyakacin bakin kokarinsa na ganin ya kawo karshen kashe-kashen.

Shin ko ka aminta cewa kashe-kashe ya yawaitane a arewacin Najeriya saboda talaucin da ake fama dashi a yankin, kuma Buhari bai yin wani abu domin taimakawa?

Shin Buharine gwamnan Kebbi, Kaduna ko Borno ko kuwa wata jiha daga jihohin arewa? Duk gwamnonin nan babu wanda baya samun tallafin kudi daga gwamnatin tarayya saboda haka kamata yayi ko wane gwamna ya magance matsalolin jiharsa da kanshi. Shi kuma Buhari a bar shi ya ji da harkokin gwmantin tarayya.

Ko kana ganin Tinubu zai samu nasara idan aka tsaidashi dan takarar shugaban kasa bayan Buhari ya kammala a 2023?

Gaskiya bana tunanin Tinubu zai mulki Najeriya. Dalili kuwa shine ‘yan kudu basu iya daukar tsawon awanni saman layi domin jefa kuri’a. Mafi yawansu kasuwancinsu ya fiye masu muhimmanci. Amma dan arewa kuwa zai iya saboda haka idan gad an arewa ga Tinubu bana tunanin Asiwaju zai kai labara gaskiya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel