Malaman sakandare sunyi zanga-zanga saboda rashin albashin tsawon wata 7 a jihar Ekiti

Malaman sakandare sunyi zanga-zanga saboda rashin albashin tsawon wata 7 a jihar Ekiti

-Daruruwan malaman sakandare sunyi zanga-zanga a dalilin rashin biyansu albashi na tsawon watanni 7

-Tsohon gwamnan Ekiti ya bar Fayemi da aikin biyan bashin albashin malamai a jihar Ekiti

Malaman sakandare a jihar Ekiti wadanda tsohon gwamnan jihar Ayodele Fayose ya dauka aiki a watan Satumbar shekarar data gabata ne suka gudanar zanga-zanga a jiya. Zanga-zangar dai ta biyo bayan rashin biyansu albashin tsawon wata 7.

Malaman sun roki gwamna Kayode Fayemi da ya tausaya masu ya biya wannan albashin da suke bi bashi domin ya share masu kukansu.

Malaman sakandare sunyi zanga-zanga saboda rashin albashin tsawon wata 7 a jihar Ekiti
Malaman sakandare sunyi zanga-zanga saboda rashin albashin tsawon wata 7 a jihar Ekiti
Asali: UGC

KU KARANTA:Abun da ya sa Buhari ba zai sauke ministocinsa ba – Lai Mohammed

Daruruwan malaman sunce fitowarsu ta kasance domin janyo hankalin gwamnati zuwa garesu. Amma sai dai kamar yinkurin nasu baiyi wani alfanu ba saboda har yanzu ba ace dasu komi ba.

Daya daga cikin masu zanga-zangar, Bayo Omoyemi, ya shaidama yan jarida cewa a madadin abokan aikinsa sun rubuta wasika zuwa ga gwamna Fayemi, matarsa, mataimakin gwamnan da kuma masu sarautun gargajiya. Inda suke rokonsu da su ceci rayuwarsu “a fiddasu daga halin ni ‘ya sun da suke ciki.”

Omoyemi ya sake cewa: “Muna son gwamnati ta kula mu domin magance mana damuwarmu. Kasancewar yanzu ana hutu, kafin a koma hutun zango na uku yakamata ayi wani abu kan wannan matsala.

“Da dama daga cikinmu basu iya biyan kudin haya a wuraren da suke zaune. Matsaloli daban-daban dai na rayuwa muke fuskanta sakamakon rashin albashin. Muna rokon gwamnati na ta dubi wannan lamarin da idon rahama ayi wani abu a kai.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel