Zan kawo karshen gabar da ke tsakanin Saraki da Tinubu – Kalu

Zan kawo karshen gabar da ke tsakanin Saraki da Tinubu – Kalu

Tsohon gwamnan jihar Abia kuma zababben sanatan Abia ta arewa, Dr. Orji Uzor Kalu yayi alkawarin sasanta Shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki da babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu.

Da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a Johannesburg, Kalu yayi alkawarin shiga tsakaninsu, inda ya bayyana cewa kada a bari siyasa ya haddasa rashin aminci a tsakanin yan uwa da abokan arziki.

Ya roki shugabannin biyu dasu janye takobinsu domin dorewar damokradiyyar kasar.

Kalu, yayinda yake jinjinawa gudunmawar da Saraki da Tinubu suka bayar wajen ci gaban siyasar kasar, ya tuna daddadiyar aminci da alakar da ke tsakanin tsoffin gwamnonin na jihohin Kwara da Lagas.

Zan kawo karshen gabar da ke tsakanin Saraki da Tinubu – Kalu

Zan kawo karshen gabar da ke tsakanin Saraki da Tinubu – Kalu
Source: UGC

Ya shawarci kafafen watsa labarai da su yi taka-tsan-tsan da nuna kwarewa wajen kawo rahoton muhimman batutuwan da suka shafi kasa, inda ya kara da cewa kada rukunin siyasa ya zama barazana ga aminci.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari zai tafi kasar Ingila a yau

Kalu, wanda ya samu rakiyan matarsa, Ifunanya, ya roki yan siyasa das u rungumi suka sannan ya roki Saraki da Tinubu da su rungumi zaman lafiya, inda ya kara da cewa shi (Kalu) ba zai saduda ba har sai ya dawo da kyakyawar alakar da ke tsakaninsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel