Sanata Barau da Buba Galadima sun ja layi kan shugabancin majalisar dattawa

Sanata Barau da Buba Galadima sun ja layi kan shugabancin majalisar dattawa

Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa lamuncewa Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Ahmad Lawan da shugabancin APC tayi domin ganin ya zama Shugaban majalisar dattawa na gaba shine shahararren hukunci da dukkanin manyan masu ruwa da tsaki na jam’ iyyar suka yanke.

Barau, wanda ke jagorantar kwamitin majalisar dattawa akan karatun jami’a, ya bayyana a wani shirin AIT, Kaakaki, wanda aka gudanar a Abuja a jiya, Talata cewa a ajiye batun lamucewa a gefe, Lawan ne sanatan APC da yafi cancanta ya riki wannan matsayi.

“Abun da jam’iyyar tayi wajen tsayar da Lawan ba hukuncin Shugaban kasa bane shi kadai, ba ra’ayin kansa bane shi kadai. Ra’ayin APC ce baki daya,” inji shi.

“Jam’iyyar ta lura cewa akwai kulli kafin zaben shugabancin majalisar dokokin kasar. Don haka sai jam’ iyyar tayi tunanin yin abunda ya kamata sannan ta zabi mutumin da ya cancanta. “Muyi abubuwa yadda yake a majalisun kasashen duniya,” inji Sanata Barau.

Sanata Barau da Buba Galadima sun ja layi kan shugabancin majalisar dattawa

Sanata Barau da Buba Galadima sun ja layi kan shugabancin majalisar dattawa
Source: UGC

“Lawan ne sanatan da ya fi cancanta saboda zai cika shekaru 20 a majalisa a ranar 29 ga watan Mayu,” inji shi.

Amma da yake Magana a wannan shirin, kakakin kungiyar kamfen din Shugaban kasa na PDP, Buba Galadima, yace koda dai Lawan ya cancanci zama Shugaban majalisar dattawa a kowani mataki, shi da PDP ba za su aminta da tursasawa ba.

KU KARANTA KUMA: Ramadan: Limaman Saudiyya za su jagoranci sallar asham a kasashe 35

“Wasu mutane za su fada maka cewa suna sin su shuka shugabanci a majalisar dokokin kasa saboda suna da wani ido a 2019. Dukkanin wadannan abubuwa na a ajiye. Babu shakka, APC na tsoro kan abunda zai faru a kotu.

“Abunda ya faru a 2015 ya rigada yana kan maimaita kansa. Bana tunanin wadan ke a jam’iyya mai mulki na tunani da kawunansu. Bamu ce komai ba. Muna dai kallo ne kawai, kuma a zauren majalisa, za mu yanke hukunci.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel