Harin Kajuru: Rundunar yan sanda ta bayyana sunan mutum na biyu da aka kashe a harin

Harin Kajuru: Rundunar yan sanda ta bayyana sunan mutum na biyu da aka kashe a harin

- Hukumar yan sandan Kadunata bayyana sunan mutum na biyu da masu garkuwa da mutane suka kashe tare da yar kasa Birtaniya a Kajuru da ke jihar

- An bayyana sunansa a matsayin ‎Mathew Danjuma Oguche wanda ke aiki da wata kungiya mai zaman kanta

- Masu garkuwan sun sanya naira miliyan 60 a matsayin kudin fansa akan mutum uku da aka sace a lokacin harin

Rundunar yan sandan jihar Kaduna a ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu ta bayyana sunan mutum na biyu da masu garkuwa da mutane suka kashe tare da yar kasa Birtaniya a Kajuru da ke jihar.

An bayyana sunansa a matsayin ‎Mathew Danjuma Oguche wanda ke aiki da wata kungiya mai zaman kanta na kasa da kasa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa masu garkuwan sun sanya naira miliyan 60 a matsayin kudin fansa akan mutum uku da aka sace a lokacin harin.

Harin Kajuru: Rundunar yan sanda ta bayyana sunan mutum na biyu da aka kashe a harin

Harin Kajuru: Rundunar yan sanda ta bayyana sunan mutum na biyu da aka kashe a harin
Source: UGC

Koda dai kakakin yan sandan jihar, DSP Yakubu Sabo, wanda ya bayyana sunan mutum da abun ya cika dashi bai bayar da cikakken bayani akan kungiyar mai zaman kanta ba.

“Sunansa Mathew Danjuma Oguche. Har zuwa lacin mutuwarsa, yana aiki ne da wata kungiya mai zaman kanta na kasa da kasa,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun dakile zanga-zangan a saki Dasuki a Sokoto

An kasha marigayi Mathew tare da yar kasar Birtaniya, Ms Foye Mooney, a daren ranar Juma’a lokacin da masu garkuwa da mutane suka kai hari sansanin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel