Arewancin Najeriya da cigaban kasar nan

Arewancin Najeriya da cigaban kasar nan

-Arewacin Najeriya na fama da talauci duk da cewa yankin nada arzikin filin yin noma

-Noma tushen arziki, shin ya batun yake a arewacin Najeriya dangane da noma

Wasu jiga-jigan mutane a arewacin kasar nan sunyi matukar kokawa bisa ga halin da yankin nasu ke ciki a halin yanzu. Da dama daga cikin manya-manyan mutanen yankin sun ta’allaka halin da yankin ke ciki bisa ga rashin tsaro dake addabar arewacin kasar.

Alhaji Aliko Dangote wanda yake shine mutum na farko a jerin attajiran Afrika yayi magana akan matsalar yankin nashi. Kungiyar dattawan arewa itama tayi magana makamanciyar tashi sannan kuma Mai martaba Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi shima yayi tashi maganar.

Arewancin Najeriya da cigaban kasar nan
Map of Nigeria
Asali: UGC

KU KARANTA:Tsohon shugaban kasar Kenya ya rasa dansa na farko

Abin zai yi matukar bada mamaki ganin cewa yankin na arewacin kasar shine a baya musamman fannin cigaba a Najeriya. Tabarbarewar cigaba da jin dadin rayuwa a wannan yankin dai ya samo asaline dalilin matsalolin tsaro da suka sa wannan yankin a gaba. Akwai matsalar boko haram, yan bindiga, rikicin manoma da makiyaya wanda ya samu shiga kasashen dake makwabtaka da Najeriya.

Dangote ya nuna rashin jin dadinsa akan cewa gaba daya jihohi 19 na arewacin kasar nan suna cikin wani hali na rashin cigaba. Dangoten yayi wannan magana ne a jihar Kaduna wajen wani taro dake tattaunawa kan tattalin arziki da kuma harkokin kasuwanci.

Ga abinda yake cewa, “Kashi 60 cikin dari na yan arewa na rayuwane cikin matsanancin talauci duk da cewa munada wadataccen fili na yin noma. Noman da inda zamu maida hankali kansa nan da shekara 10 zai samar mana kudaden shiga wanda ma yafi na man fetur."

A cewar sauran masu jawabi irin nashi, yankin arewa na fama da talauci kuma hakan dai ya biyo bayan sakaci da mugunta ne daga wajen gwamnoninmu. Akasarinsu sata kawai da handamar dukiyoyin jama’a ke gabansu. Wannan shine dalilin da yasa yankin namu bai cigaba kana kuma talauci da jahilci ke damun mutanenmu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel