Da duminsa: Kasar Dubai ta yankewa yan Najeriya 8 hukuncin kisa

Da duminsa: Kasar Dubai ta yankewa yan Najeriya 8 hukuncin kisa

An yankewa yan Najeriya hukuncin kisa a garin Sharjan, kasar UAE kan laifin fashi da makamin da sukayi a watan Disamban 2016.

Wannan hukunci na zuwa ne jim kadan bayan an damke wasu yan Najeriya biyar da suka kai harin fashi da makami kasuwa canji a Dubai.

Game da cewar jaridar Gulf, Alkali Majid Al Muhairi na kotun Sharjah ya yanke hukuncin cewa bayan an tabbatar da laifin da mutanen da ake zargi da yi na fashi da makami a kasuwanni canji da na'urar cire kudi wato ATM a kasar Dubai a shekarar 2016.

Jimillan mutane 20 aka damke da farko kan laifin kai hari kan jami'an tsaro dake raka motocin kudi zuwa na'uarar ATM hari a garin Sharjah. Gungun wadanda suka kai wannan hari sun kawo ziyara kasar ne kawai.

KU KARANTA: Jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ta dauki fasinjoji 1.5m cikin kwana 1,000

Daga cikin mutane 20, an tabbatar da zargi kan tara kuma an yankewa takwas hukuncin kisa. Na taran ya samu hukuncin watanni shida a gidan yari sannan a koreshi daga kasar kan laifin mallakan kudin sata.

Rahoto ya nuna cewa sun saci kudi Dh1,700,000 (N166.,613,352.21), wannan kudin da aka samu a hannunsu kenan bayan sun raba sauran tsakaninsu kudin kuma sun tura Najeriya.

Jakadan Najeriya a kasar UAE, Mohammed Rimi, ya ce yan Najeriya 446 na kurkukun kasar a yanzu kan laifuka daban-daban da ya hada da safarar muggan kwayoyi da fashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel