Zababbun yan majalisa 164 sun bayyana goyon bayansu ga Femi Gbajabiamila

Zababbun yan majalisa 164 sun bayyana goyon bayansu ga Femi Gbajabiamila

Zababbun yan majalisar wakilan tarayya karkashin inuwar jam'iyyar All Progressives Progress (APC) a ranar Alhamis sun alanta goyon bayansu ga shugaban masu rinjaye a majalisa, Femi Gbajabamila matsayin kakakin majalisa.

Kungiyar yan majalisan da ya kunshi mutane 164 sun ce ba zai dace a zabi shugaban kasa dan Arewa, shugaban majalisar dattawa dan Arewa, sannan kakakin majalisar wakilai shima dan Arewa ba.

A wani jawabin da suka gabatar ta bakin shugaban kungiyar, Hanarabul Tunji Olabunmi Ojo da diraktasu, Dunkwu Nnamdi Chamberlain, zababbun yan majalisan APC a majalisar wakilai sunce abun da kamar wuya su sabawa jam'iyya da shugaba Muhammadu Buhari.

Game da cewar kungiyar, jam'iyyar ta baiwa Arewa kujerar shugaban kasa, ta baiwa kudu kujerar mataimakin shugaban kasa, ta baiwa arewa kujerar shugaban majalisar dattawa, sannan ta baiwa kudu kujerar kakakin majalisar wakilai.

Sunce mutanen Arewa maso tsakiya masu ikirarin cewa lallai a basu kujerar kakakin majalisa ba su son gaskiya saboda ba zai yiwa Arewa ta fitar da shugaban kasa da shugabannin majalisun guda biyu ba.

KU KARANTA: Hukuncin Onnoghen nasara ce ga yakin cin hanci da rashawa - Fadar shugaban kasa

Kana abinda ya kamata shine dukkan yan majalisa APc su yiwa jam'iyyar biyayya kan abinda ta zaba.

A bangare guda, A daren jiya Alhamis, fadar shugaban kasa ta yi tsokaci kan hukuncin da kotun CCT yanke kan tsohon shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen, inda ta ce wannan babban nasarace ga kudirin gwamnatin shugaba Buhari.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa sakamakon shari'ar Onnoghen ya nuna cewa babu ruwan doka da girma kujerar mutum ko matsayinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel