Sarakunan Zamfara sun saki jerin sunayen jama'ar gari da harin Soji ya kashe

Sarakunan Zamfara sun saki jerin sunayen jama'ar gari da harin Soji ya kashe

Majalisar sarakunan jihar Zamfara sun mayar da martani kan kalubalen da hukumar Sojin saman Najeriya tayi musu na cewa su bayyana sunayen wadanda sarakunan ke ikirarin cewa harin jiragen soji kan yan bindiga ya kashe.

A jiya Laraba, 17 ga watan Afrilu, majalisar sarakunan sun saki sunayen mutane garin da harin ya kashe 11 yayinda aka kaiwa yan bindiga harin a karamar hukumar Zurmi.

Sunayen sune:

Mai Daji Barau,

Na Dumburum,

Suwaiba Alka,

Yar Guru Na Dumburum,

Maryam Shafiu,

Dahe Malan Sule,

Buhari Dan Kurma,

Zaliha na Dumburum,

Aisha Akilu,

Alamin Alka

Fati ‘Yar Gum.

Game da cewar sarakunan, wasu mutane 11 sun samu raunuka sakamakon wadannan hare-hare a garin Dumburum, karamar hukumar Zurmi na jihar ranar 9 ga watan Afrilu, 2019.

Sunayen wadanda suka samu raunukan sune:

Haruna Kusu,

Muhammad M Sani,

AbdulRazak Abubakar,

Yakubu Yunusa,

Dan Diyya,

Sa’a Dayyabu,

Yar’wargi Mamman,

Gwamna na Dumburum,

Rashida Alka,

Maryam Akilu

Sadiq Sukuranu.

Kana sun ambaci cewa akwai mutane 20 da aka harin ya rusawa muhalli.

A hira da manema labarai da suka gabatar a Gusau, Wakilin sarakunan jihar, Sarkin Fulanin Bungudu, Alh Hassan Attahiru ya jaddada cewa hari sojin ya kashe al'ummar gari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel