Mutum hudu sun mutu a kamfanin narka karfe na Indiya dake jihar Ogun

Mutum hudu sun mutu a kamfanin narka karfe na Indiya dake jihar Ogun

-Ma'aikata sunyi bore sakamakon mutuwar ma'aikata hudu na wani kamfanin narka karfe

-Ma'aikatan kamfanin sun koka sakamakon mawuyacin halin da suke ciki, kamfanin sam bai masu abinda ya dace domin karfafa masu gwiwa akan aikin nasu

Wata zanga-zanga ta barke a sararin kamfnin narka karfe mallakar kasar Indiya mai suna, ‘African Foundries Limited’ dake kan hanyar Shagamu zuwa Ikorodu a jihar Ogun bayan da mutum hudu suka mutu yayinda narkakken karfe ya zubo musu.

Abokan aikinsu ne suka gudanar da wannan zanga-zanga, yayinda suka bayyana ma yan jarida cewa babu kyakkyawan yanayin aiki, babu albashi mai kyau sannan kuma da yinkurin rufe wannan mutuwar da hukamar kamfanin tayi, sune dalilan da suka sa muke wannan zanga-zanga.

Steel company

Steel company
Source: UGC

KU KARANTA:Ma’aikata sun roki Buhari da ya sa hannu akan sabon karancin albashi

Wakilinmu wanda ya samu damar ziyartar wannan wuri ranar Litinin, ya tararda manya-manyan motaci dauke da raftar karafuna da dama a waje an hanasu shiga cikin kamfanin. Dakin da ake zama domin tarbar baki yayi matukar lalacewa, cike yake da gilasai wadanda suke fassasu daga kofa da kuma taga ta dakin.

Wasu daga cikin ma’aikatan sun shaida ma wakilinmu cewa, kamfanin yace da su kada su fadawa jama’a labarin abinda ya faru. Sun sake cewa, an ce dasu su tafi gida ha zuwa ranar Talata. Sai dai kuma babu wani yinkurin da kamfanin keyi domin kulawa da iyalan wadanda suka rasun.

Akwai daya daga cikin ma’aikatan wannan kamfanin da karya dokar tasu inda yayi magana da yan jarida, ya shaida mana cewa ko kadan basu jin dadin aiki da kamfanin saboda haka nema zaka samu ilahirin ma’aikatan wurin na kuka da wannan kamfani.

Yace da yawanmu mun kasance muna aiki a wannan wuri tsawon shekara 13 kenan yanzu, amma basu bamu damar zama hakikanin ma’aikatan wannan wuri ba. A duk lokacin da iftala’i ya afkawa daya daga cikin ma’aikatan sai kamfanin ya ki daukar yin shi inda kamfanin ke fakewa da ai ba ma’aikacin gaskiya bane hayar shi aka dauka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel