Wata amarya yar shekara 15 ta saka ma mijinta gubar bera a abinci

Wata amarya yar shekara 15 ta saka ma mijinta gubar bera a abinci

Hukumar yan sanda jihar Kano sun kama wata amarya yar shekara 15 mai suna Hassana Lawan, yar kauyen Bechi, a karamar hukumar Kumbotso da laifin saka ma mijinta mai suna Sale Abubakar mai kimanin shekara 33 guba a abincinsa.

Jami’in hulda da jama’a, na hukumar, DSP Abdullahi Haruna ya tabbatar da labarin ne a wani sanarwa da ya bayyanawa manema labarai a Jihar kano ranar Talata.

Haruna ya bayyana cewa ranar talata da misalin karfe 2 na rana, Yan sanda suka samu labarin cewa wadda ake zargin ta saka ma mijinta gubar bera a abincinsa.

Yace an kai mijin asibitin Murtala Muhammad dake jihar domin magani.

KU KARANTA: Tsaffin shugabannin majalisa 2, tsohon kakakin majalisar wakilai, tsaffin gwamnonin PDP sun marawa Ahmad Lawan baya

Jami’in hulda da jama’a ya bayyana cewa yan sanda sun fara bincike akan al’amarin kuma za'a shigar da kara zuwa kotu da zaran an kammala binciken.

A wani labarin mai kama da haka, Wani magidanci, Daniel Okafor, mai matsakaitan shekaru ya kashe kan sa bayan an yi zargin cewar ya watsa wa matar sa wani wani ruwa mai guba a garin Nsugbe da ke jihar Anambra.

Marigayin, dan asalin garin na Nsugbe, ya hallaka kan sa ne da misalign karfe 2:30 na dare bayan ya kwankwadi ruwan gubar da ya kwara wa matar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel