Fashi: Ministan tsaro yace furucinsa baya nufin kaskanta sarakunan gargajiya

Fashi: Ministan tsaro yace furucinsa baya nufin kaskanta sarakunan gargajiya

Ministan tsaro, Mansur Dan-Ali, ya bayyana cewa furucin da yayi na zargar wasu sarakunan gargajiya a arewa maso yamma da hannu a ayyukan yan bindiga ba wai don kaskantar da martabarsu bane.

A wani jawabi a ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilu daga bakin kakakin Ministan, Kanal Tukur Gusau yace, “An jawo hankalin Ministan Tsaro akan rubuce rubucen wasu kafofin labarai dake zargin cewa ya zargi wasu sarakunan gargajiya da hada baki da yan bindiga a jihohin dake fuskantar hare-hare.”

Yace, “Don cire shakku, jawabin ba yana nufin kaskantar da manyan sarakunan gargajiya a jihohin da abun ya shafa bane.”

Fashi: Ministan tsaro yace furucinsa baya nufin kaskanta sarakunan gargajiya

Fashi: Ministan tsaro yace furucinsa baya nufin kaskanta sarakunan gargajiya
Source: UGC

Gusau ya kara da cewa, “jawabin gargadi ne ga wasu shugabanni da mutanensu."

A ranar Talata da ya gabata ne, Ministan Tsaro Mansur Dan-Ali yace wasu sarakunan gargajiya sun kasance daga cikin masu taimaka ma yan bindiga da rahoton kwararru wajen gudanar da ayyukan garkuwa da mutane wanda hakan yana tabarbarar da shirye-shiryen ayyukan rundunar soji a yankin Arewa maso Yamma.

A kwanan nan ne rundunar soji da yan sanda suka kaddamar da ayyukan tsaro don yaki da masu garkuwa da mutane da kuma yan bindiga da suka addabi kauyuka da al’umma a wasu jihohin Arewa maso Yamma, ciki harda jihohin Kaduna, Niger, Zamfara, Plateau da Katsina.

An kaddamar da ayyukan ne don yaye ayyukan da yan bindiga da masu laifi ke gudanarwa a yankin Arewa maso Yamma. Rundunar sojin sama har ila yau ta karfafa hare-hare akan yan bindiga a Zamfara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel