Takardar shaidar Firamare kadai mutum ke bukata domin takarar shugaban kasa - Babban Lauya

Takardar shaidar Firamare kadai mutum ke bukata domin takarar shugaban kasa - Babban Lauya

Jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP da dan takararta, Atiku Abubakar, sun shigar da kara kotu kan cewa shugaba Muhammadu Buhari bai da takardan shaidar WAEC kuma saboda haka, bai cancanci yin takara a zaben shugaban kasa ba.

Hakan ya jawo cece-kuce tsakanin lauyoyi da masu sharhi kan al'amuran yau da kullum inda ake tambayar cewa shin me kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada kan darajar ilimin da mutum zai kai kafin ya iya takara kujeran shugaban kasa.

Babban lauya kuma kakakin yakin neman zaben jam'iyyar All Progressives Congress APC, Festus Keyamo, ya bayyana cewa ba takardan darajar ilimi bane kadai abinda zai iya sa mutum cancantan takara.

Ya ce dadewa a gwamnati na tsawon shekaru akalla goma zai iya ba mutum daman takara.

KU KARANTA: An ga sanannun yan bindiga a gidan bikin 'yayan Sarkin Zurmi kuma sun bada gudunmuwa

Yace: "Akwai wasu darajoji da zasu iya baiwa mutum daman takara kujeran shugaban kasa. Kana, idan ka taba rike kujerar gwamnati na tsawon wani lokaci kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, ba ka bukatan WAEC domin zama shugaban kasa."

"Sashe na 318 na kundin tsarin mulkin 1999 ya yi ta'arifin takardar karatu matsayin shaidar kammala ajin Firamre na 6, iya magana da turanci, iya rubutu, iya fahimtar yaren Turanci. Ba'a bukatar takardar WAEC."

A bangare guda, jam'iyyar APC ta bayyanawa kotu cewa abokin hamayyar shugaba Buhari a zaben 2019, Atiku Abubakar, ba haifaffen dan Najeriya bane, saboda haka bai cancanci takara a zaben ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel