Zamfara: Sakamakon harin Soji, yan bindigan sun dawo cikin gari - Mazauna sun laburta

Zamfara: Sakamakon harin Soji, yan bindigan sun dawo cikin gari - Mazauna sun laburta

A yanzu haka, wasu yan bindigan da suka addabi jihar Zamfara sun dawo cin karansu ba babbaka a cikin garururuwan karamar hukumar Zurmi na jihar bayan hukumar soji ta fara kai hare-hare dazukan da yan bindigan ke boyewa.

Wasu mazauna garin sun bayyana cewa tun lokacin da soji suka fara kai hare-hare cikin dazuka, yan barandan jihar sun guje daga dazukan zuwa cikin gari.

KU KARANTA: Rikicin Zamfara: An ga sanannun yan bindiga a gidan bikin 'yayan Sarkin Zurmi kuma sun bada gudunmuwa

Daya daga cikin mazaunan wanda aka sakaye sunansa yace: "A yanzu da nike muku magana, ana ganin yan bindiga a garuruwan Jaja, Rukudawa da Tsanu, dukka a karamar hukumar Zurmi; suna yawonsu da bindigoginsu rataye a kafada basu tsoron kowa."

"Yan bindigan suna zuwa shaguna suna siyayya irin Maltina, Madarar gwangwani, da Nama. Suna cin karansu ba babbaka. Babu wanda ke da karfin halin da zai musu kallon banza. Suna da idanuwa a cikin garin."

"Suna zaune da su ko su fito daga cikin daji zuwa wadannan garuruwa su kwana."

Mazaunin yace harin jami'an sojin saman da aka kai Dumburum ya yi tsanani kan yan bindigan kuma hakan ya tilasta musu guduwa daga daji.

Amma hakan bai isar ba, saboda a karamar hukumar Zurmi, babu sojoji a kasa, hakan ya ke sa yan bindiga yawonsu cikin gari ba tare wani ya tsaresu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel