Sakkawato: Birnin Shehu; inda yara kanana ke fita domin neman aikin yi

Sakkawato: Birnin Shehu; inda yara kanana ke fita domin neman aikin yi

- Matasa da yara kanana ba a barsu baya ba suma wajen neman na kansu duk da kuwa makarantar da suke zuwa

- Su kuwa wasu yaran sun gwammace su yita zuwa yawon banza a maimakon su je suyi wani aiki mai wahala

Mafi yawan yaran sun taso gidajen dake da karamin karfi saboda haka iyayensu basu iya daukan nauyinsu. Wannan dalilin ne yasa akasarin yaran suke fita neman aiki domin samun dan abinda zasu magance matsalar kansu. Akan wannan batu ga rubutun da Adelani Adepegba yayi, wanda ya ziyarci birnin Sakkawaton kwanan nan.

Mustafa Aminu mai shekaru 13, yana tsakiyar aiki mai wuya cikin rana inda ya kasance yana zuba yashi a cikin motar dake daukan yashin a Gangeru Tashar Illela dake Sakkwato, yayinda wakilinmu ya hangeshi. Daga kallonsa kasan a gajiye yake sai dai kawai ya dake yana aikin ba tare da nuna cewa ya gaji ba. Abokin aikinsa kuwa mai suna, Abdulmalik Usman dan shekara 20 wanda ya kasance yana wannan aikin tun yana dan shekara 17 shima din yana nashi aikin. Shi kuwa Aminu watan shi hudu kawai da fara aikin inda ya shaida mana cewa yana samun naira dari biyar (N500) a kowace rana.

Matasa a bakin aiki

Matasa a bakin aiki
Source: UGC

KARANTA WANNAN:Hanashi takarar gwamna: Kotu ta yi watsi da karar da Ministan sadarwa, Shittu ya shigar kan APC

Matashin ya bayyana mana cewa, a ko wace rana yana cika motar diban yashi takwas zuwa tara, ya sake cewa ya zabi yin wannan aikin ne domin ya samu kudi a maimakon ya rinka zuwa ‘yawon banza’. A kulli yaumin ina samun naira dari biyar wanda nake baiwa Hajiya (mahaifiyarsa) ajiya.

“Ina zuwa wajen aikin ne kullum idan na dawo daga makaranta. Aikin nan da nake yafi mani yawon banza kamar yanda wasu abokaina ke yi”. A cewarsa da yawa daga cikin abokansa ba son aikin sukeyi ba saboda wahalarsa. Aminu wanda ke da burin zama Lauya a nan gaba, yana zuwa firamare a halin yanzu inda yake aji biyar. Sai dai kuma duk da haka ya kasa yi mana magana cikin harshen turanci sai da wani yayi tafinta tsakaninshi da wakilinmu.

Usman kuwa, wanda yayi ikirarin cewa yana aji uku a matakin karamar sakandare (JSS 3), ya mana bayanin cewa ya kwashi tsawon shekara uku yana yin wannan aiki kuma hakika aikin yana matukar taimakamasa.

“Iyayena sun so su hana ni wannan aikin saboda wahalarsa, amma nayi kokarin fahimtar dasu cewa ta sanadiyar aikin nan da nake yi ina samun daman taimaka masu daga dan abinda nake samu nima.” Dan shekara 20 da haihu, Usman ya bayyana mana kudrinsa na son zama soja a nan gaba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel