Mijina ya fi daukar dawainiyar mahaifiyarsa fiye da ni da 'yayana

Mijina ya fi daukar dawainiyar mahaifiyarsa fiye da ni da 'yayana

Wata mata ta kawo kuka yanar gizo kan abinda take ganin rashin adalci ne da mijinta yake yi na fifita mahaifiyarsa kan ita da kuma 'ya'yanta.

Tana neman shawararku kan abinda kuke ganin ya fi dacewa tayi a wannan hali da take ciki. Karanta jawabinta:

"Bansan ko ni na dauki wannan abun da muhimmanci ba. Yau shekara na hudu da aure da yaya biyu, wannan ce matsala: Lokacin da na hadu da mijina, munyi zawarci na tsawon shekara biyu kafin muyi aure, lokacin da muka hadu sai na fuskanci baya zuwa ya ga iyayensa, sai na tambaye shi dalilin hakan,sai yace mahaifiyar shi tana da matsaloli da yawa, sai na nuna mai cewa uwa, uwa ce komin rintsi, daganan na lallabe shi ya koma wurin iyayensa.

"Tun lokacin da muka yi aure sai na fahimci abinda yasa mijina baya zuwa wurin mahaifiyarsa saboda ta kasance tana tatikan mijina kamar yana baro kudi ne a bishiya. Mijina ya kasance yana dawainiya da mahaifiyarsa, mahaifinshi da sauran yan uwansa sosai."

"Sirikata ta kasance tana aiki, kuma tana amsar albashi, amma idan iskar gas dinsu na girki yakare, sai fadawa mijina ya cika musu, ya kasance shi ke biya musu kudin haya, kuma shi yake biyan kudin makarantar kannenshi guda biyu, yana daukan dawainiyar mahaifiyarshi fiye da ni da yayana."

Na kira shi a waya ba sau daya ba akan ina yake tunanin zan samo kudin da zan dauki dawainiyar iyalina da gidana, sai ya dan tsakuro kudi ya bamu amma kowani sati mahaifiyar shi tana amsar makudan kudi a wurin shi.

Ina neman shawararku ko menene mafita?"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel