Gwamnatin tarayya zata tilastawa masu gidajen man fetur siyar da gas din girki

Gwamnatin tarayya zata tilastawa masu gidajen man fetur siyar da gas din girki

-Za a fara siyar da gas din girki a gidajen man fetur

-Akwai yiwuwar fara samun gas din girki a gidajen siyar da man fetur

Gwamnatin tarayya ranar Alhamis ta bayyana cewa zata bi tsarin dokokin majalisa hanyar sashen kula da ma’adanai da suka shafi man fetur wato DPR ‘Department of Petroleum Resources’ a turance domin tursasa masu kasuwancin man fetur domin suyi tanadin siyar da gas din girki a gidajen man dake fadin kasar.

Karamin Ministan man fetur, Ibe Kachikwu shine ya fadi hakan, a Abuja yayin da yake kaddamar da bude ‘Nigerian Army Welfare Limited by Guarantee’ NAWLG, kamfanin mu’amala da gas ta kasa a barikin Mambilla da ke Abuja kuma ya bude kananan wurraren wannan muhummin abu domin ya samu kaiwa ga kowa musamman jami’an sojin dake wata barikin ta daban.

NNPC station
NNPC station
Asali: Depositphotos

KU KARANTA:Harin rundunar sojin sama alummar gari kawai ta kashe ba yan bindiga ba

Kachikwu yace wannan umurni ya biyo bayan matukar amfanin gas din a fadin kasar nan, bugu da kari da kuma amfani da tsaftataccen sinadari domin ganin cewa ya kawo hanyar samar da aikin yi domin a rage zama banza.

A wani labarin kuwa, hukumar INEC ta lashi takobin cewa lallai ba zata baiwa gwamanan jihar Imo, Rochas Okorocha takardar shahadar nasara a zaben majalisar dattawa ba.

Hukumar ta INEC tace sam Okorocha ba zai samu takardar shahadar ba daga wurinta saboda wasu hujjoji da take dasu akan gwamnan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel