Wata mata mai noman tumatur zata bude kamfanin sarrafa tumaturin a Kaduna

Wata mata mai noman tumatur zata bude kamfanin sarrafa tumaturin a Kaduna

-Kamfanin zai samar da tumaturin a cikin bokiti har ma da na cikin duro babba wanda masu bukatarsa da yawa kan iya siya.

- Zan bude kamfanin markaddaden tumatur nan da tsakiyar shekara mai zuwa

Mira Metha, shararriyar mai noman tumatur da kimanin eka dari biyar dake kusa da Kangimi dam na jihar Kaduna tana shirin shigowa kasuwar sarrafa tumatur da zafinta ta hanyar bude nata kamfanin nan da watanni masu zuwa.

Malama Metha ita ce mai kamfanin tumatur dake Jos. Ta shaidawa jaridar Daily Trust a gonarta dake Kangimi dam cewa tayi niyyar sake bude wani sabon kamfanin sarrafa tumatur wanda taso yi tun tsakiyar shekarar bara (2018) amma hakan bai yiwu ba.

Tomato paste

Tomato paste
Source: UGC

KARANTA WANNAN:2019 Hajj: Birnin Tarayya ta fara taron wayar da kai ga maniyata

Ranar Litinin 8 ga watan Afrilu, tayi magana akan shafinta na sadarwa wato twitter ga kuma abinda ta sanar: “Labari mai kayatarwa! A wannan makon kamfanin Jos zai sarrafa kashi na farko na markadadden tumatur domin gwajin da muke gabtarwa domin shiryawa kakar shekarar 2020.

"Bamu gama fitar da tsarin yanda zamu sayar da wannan tumatur ba tukun amma dai zamu siyar da kilo 25 a bokiti da kuma kilo 250 a cikin duro. Ko wane bokiti zai kama naira dubu bakwai da dari biyar.”

“Duroruwan za a saidawa manya yan kasuwa inda kuma na bokitin za a siyarwa masu siya domin suyi amfani dashi. Ba zamu iya saidasu yanzu ba sai dai zamu iya sa gishiri a cikin kowane bokitin domin ya tsare tumatur din cikin yanayi mai kyau har na tsawon mako biyu ba tare da an sa cikin na’urar firij ba."

“Tumatur din zai kasance ana sarrafa shi tare da gishiri don bashi kariya kana kuma ya za aiya ajiyeshi har na tsawon lokaci ba tare da ya lalace ba” ta kara jaddadawa cewa gishiri zai bawa tumaturin kariyar tsawon mako daya zuwa biyu amma dai abu mafi kyawo shine a sa shi cikin firij.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel