Wani dan kasar Italiya ya kashe wata karuwa yar Najeriya saboda da gaza gamsar dashi

Wani dan kasar Italiya ya kashe wata karuwa yar Najeriya saboda da gaza gamsar dashi

-Har wa yau, wata majiyar ta tabbatar da cewa wannan danyen hukunci ya biyo bayan rashin gamsar dashi da Benedicta ba tayi ba.

-Yan sandar Italiya sun cafke Scalici kuma sun tsare shi bayan ya amsa cewa ya aikata wannan laifin da kansa.

Dan kasar Italiyan mai suna, Leopoldo Scalici, mai shekaru 41 ya shiga hannun hukuma saboda zarginsa da ake na kashe wata karuwa yar kasar Najeriya mai suna Benedicta inda ya kasheta kuma ya jefa gawarta cikin shadda.

Zance daga sashen yanar gizo na kasar Italiya na nuna mana cewa, a yau din nan ne Scalici ya nemi Benedicta a kan titin Modena Nord da tazo ta kwana a wajensa har zuwa karshen mako.

KU KRANTA:Atiku ya karyata jita-jitar da ake yadawa a kanshi

An samu labarin mutuwarta ne bayan rahoto ya tabbatar mana cewa su biyun sun kusanci juna daga bisani kuma cacar baki ta barke tsakaninsu hakan yasa Scalici ya nemi wani abu mai kaifi ya doketa dashi a fuska.

Har wa yau, wata majiyar ta tabbatar da cewa wannan danyen hukunci ya biyo bayan rashin gamsar dashi da Benedicta ba tayi ba.

Yan sandar Italiya sun cafke Scalici kuma sun tsare shi bayan ya amsa cewa ya aikata wannan laifin da kansa.

Akwai shirin yin bincike akan musabbabin mutuwarta.

A wani labarin kuma, hukumar INEC ta lashi takobin cewa ba zata baiwa gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, takardar shahadar nasara azaben majalisar dattawa ba.

Hukumar ta INEC tace, lallai ba zata baiwa Okorocha takardar shaidar lashe zaben majilisar dattawa ba saboda akwai hujjojin da ta rike na yin hakan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel