Mu leka kotu: Ina da shekaru 11 Baba 90 ya fara lalata da ni - Yar shekaru 13

Mu leka kotu: Ina da shekaru 11 Baba 90 ya fara lalata da ni - Yar shekaru 13

- Wata yarinya mai shekaru 13 ta labartawa kotu yadda wani mai shakru 60 ya yi lalata da ita a lokacin ta na da shekaru 11

- Dalibar ta shaidawa kotun cewa Ali ya dauke da karfin tsiya ya kaita wani gida da ba a kammala ba, inda ya yi lalata da ita a cikin watan Fabreru, 2017

- Mai shari'ar, Sybil Nwaka ya dage sauraron karar har sai ranar 14 ga watan Mayu

Wata yarinya mai shekaru 13 (wacce aka boye sunanta), ta labartawa kotun sauraron kararraki na musamman da cin zarafi da ke Ikeja yadda wani mai shakru 60, wanda kuma ya kasance abokin kasuwancin kakanta ya yi lalata da ita shekaru biyu da suka gabata a lokacin ta na da shekaru 11.

Yarinyar ta bayyana hakan a ranar Talata a yayin da ake sauraron shari'ar wani mai suna Ahmadu Ali da aka fi sani da 'Baba 90', mai shekaru 62 a yanzu, bisa zarginsa da cin zarafi.

A yayin da jami'i mai shigar da kara, Mr Babajide Boye, ya gabatar da ita a matsayin shaida, dalibar ta shaidawa kotun cewa Ali ya dauke da karfin tsiya ya kaita wani gida da ba a kammala ba, inda ya yi lalata da ita a cikin watan Fabreru, 2017.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Rundunar soji ta yi arangama da mayakan Boko Haram kan hanyar Damaturu-Maiduguri

Mu leka kotu: Yadda wani magidanci ya yi lalata da ni ina da shekaru 11 - Yar shekaru 13

Mu leka kotu: Yadda wani magidanci ya yi lalata da ni ina da shekaru 11 - Yar shekaru 13
Source: Twitter

"Kakata ta aike ni na kaiwa 'yar uwata auduga. A kan hanyata ta dawowa, Baba 90 ya jani da karfin tsiya ya shigar da ni wani kango. Na sanshi, yana sayan kayayyaki a shagonmu.

"Ya fara ciremun kayan jikina kana ya cire nasa, inda ya sanya azzakarinsa a cikin farjina, kuma ya ce idan na gayawa wani to zai kashe ni. Wannan shi ne karo na biyu da ya yi mun hakan, na farko ya faru ne a gidanmu, a nan ma ya ce idan na sanar da wani sai ya kashe ni," a cewar ta.

Dalibar ta ce mutanen da suka ga lokacin da Baba 90 ya ja ta da karfin tsiya zuwa wannan kangon, sune suka garzaya ofishin hukumar da ke yaki da tu'ammali da muggan kwayoyi (NDLEA) domin shigar da rahoto.

"Jami'an NDLEA ne suka zo kangon suka kwashemu gaba daya zuwa ofishin rundunar 'yan sanda. Sun yi mani tambayoyi, haka shi ma sun yi masa. Kakata da mahaifiyata na a ofishin 'yan sandan a lokacin."

Kamfanin dillanci labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa, wanda ake karar ya aikata laifin ne da misalin karfe 2 na rana a ranar 2 ga watan Fabreru, a bayan ofishin hukumar NDLEA, Kasoleri, titin Itokin, Ikorodu, jihar Legas.

Mai shari'ar, Sybil Nwaka ya dage sauraron karar har sai ranar 14 ga watan Mayu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel