Jiragen ruwa 6 makare da man fetur da sauran kayayyakin amfani sun iso tashar jirgin ruwan Lagas

Jiragen ruwa 6 makare da man fetur da sauran kayayyakin amfani sun iso tashar jirgin ruwan Lagas

- Jiragen ruwa tara makare da kayayyakin amfani daban-daban na shirin sauka a tashoshin jiragen ruwan Apapa da Tin-Can Island

- Hukumar tashoshin ruwan Najeriya ce ta sanar da hakan a ranar Talata

- Hudu daga cikin jiragen shida na dauke da man fetur yayinda sauran biyun ke dauke da daskararrun kifi

Rahotanni sun kawo cewa jiragen ruwa tara makare da kayayyakin amfani daban-daban na shirin sauka a tashoshin jiragen ruwan Apapa da Tin-Can Island, hukumar tashoshin ruwan Najeriya (NPA) ta bayyana hakan a ranar Talata, 9 ga watan Afrilu a Lagas.

An tattaro cewa hudu daga cikin jiragen shida na dauke da man fetur yayinda sauran biyun ke dauke da daskararrun kifi.

Jiragen ruwa 6 makare da man fetur da sauran kayayyakin amfani sun iso tashar jirgin ruwan Lagas
Jiragen ruwa 6 makare da man fetur da sauran kayayyakin amfani sun iso tashar jirgin ruwan Lagas
Asali: UGC

Hukumar ta NPA ta kuma bayyana cewa ana sa ran jiragen kasa 26 dauke da alkama, daskararun kifi, kwantana, mai, kayayyaki, siga da fetur za sui so tashoshin ruwan a tsakanin ranar 9 ga watan Afrilu da kuma 28 ga watan Afrilu.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Najeriya ta daura laifin rikicin arewa kan sarakunan gargajiya

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, Majalisar dattawa ta bayyana cewa kudurin da za a gabatar da bunkasa harkar noma a kasar nan zai taimaka mutuka wurin habaka tattalin arziki, sannan zai taimakawa manoma da kayan aikin irin na zamani.

A jiya Litinin ne 'yan majalisar dattawa, suka tabbatar da cewa idan kudurin bunkasa harkar noma a kasar nan ya tabbata, zai kawo cigaba sosai ga tattalin arzikin kasar nan.

A cewar Sanatocin, idan kudurin ya tabbata, zai bayar da hanyar fara noma na zamani a fadin kasar na, musamman ma wuraren da suke da kasar noma mai kyau.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel