Kada ku sake biyan wani kudin fansa - Hamshakin Dan kasuwan da akayi garkuwa da shi ya bayyanawa iyalansa

Kada ku sake biyan wani kudin fansa - Hamshakin Dan kasuwan da akayi garkuwa da shi ya bayyanawa iyalansa

Alhaji Usman Mayo, babban dan kasuwan da aka biya kudin fansarsa N100million amma har yanzu ba'a sakeshi ba ya bayyanawa iyalansa cewa kada su sake baiwa masu garkuwa da mutanen wani kudin fansa.

An samu labarin cewa masu garkuwa da mutanen sun tilasta masa kiran iyalansa ta wayan tarho domin kara biya wani kudi N100,000 miliyan domin a sakeshi.

Kawai sai Alhaji Usman Mayo ya fadawa iyalansa a gaban masu garkuwa da mutanen cewa kada su sake biyan taro ko sisi daya.

KU KARANTA: Jirgin kasa ya murkushe mabaraci har lahira

Wani majiya da ke kusa da iyalin, Malam Ibrahim ya bayyanawa Daily Trust cewa Alhaji Mayo wanda shahrarren dan kasuwa ne aTakum, jihar Taraba ya bukaci mahaifiyarsa ta yafe masa saboda ya gwammace ya mutu hannun yan bindigan da ya umurci iyalansa su kara biyan wani kudin fansa.

Yace: "Ku taimaka kada ku sayar da wani dukiya nawa domin kara baiwa masu garkuwan nan kudi; na shirya mutuwa. Ku bari su kasheni idan suna so."

An tattaro cewa dan kasuwan garin Takum ya shiga hannun masu garkuwa da mutane ne a wata MAris kuma tuni iyalinsa sun biya N100 millio amma suka ki sakinsa.

Iyalin sun fidda rai cewa an kasheshi kawai sai suka samu kiransa ranar Lahadi.

Yayinda aka tuntubi kakain hukumar yan sandan jihar Taraba, DSP David Misal, ya ce bai da masaniya kan halin da ake ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel