Yadda aka ci mutuncin mata a zaben 2019 - Yan takara mata

Yadda aka ci mutuncin mata a zaben 2019 - Yan takara mata

- Wata 'yar takarar sanata a jihar Oyo ta ce sun ga yadda aka tayar da rikici, da yadda jami'an tsaro suka ci karensu ba babbaka a zaben 2019 da ya gabata

- Haka zalika, Mrs. Christina Ude, a jihar Imo, ta ce ta fuskanci jerin barazana kwanakin kadan kafin zabe

- A nata bangaren, Mrs. Phina Kanu wacce ta yi takara a majalisar dokokin jihar Abia ta ce anci zarafinta a yayin da ta je kad'a kuri'arta

Wata 'yar takarar sanata karkashin jam'iyyar PDP a jihar Oyo kuma tsohuwar shugabar masu rinjaye a majalisar tarayya, Mrs Mulikat Akande Adeola, ta ce mata na yin dukkanin abubuwan da suke ganin dai-dai ne.

Akande, wacce ta so wakiltar mazabar Oyo ta tsakiya a zaben 2019 da ya gabata, ta ce a shirye take kuma har ta samu nasarar lashe zaben fitar da gwani a cikin jam'iyyarta ba tare da samun wata matsala ba.

"A yayin gudanar da zaben 2019, kowa ya shirya yin duk mai yiyuwa. Munga yadda aka tayar da rikici, munga yadda jami'an tsaro suka ci karonsu ba babbaka, tare da aringizon kuri'u da dai sauran su. Ni ce yar takarar da ta fi kowa nasibi, amma hatta su kansu 'yan mazaba ta sun yi mamakin yadda aka ce ba ni ce na lashe zaben ba," a cewarta.

KARANTA WANNAN: Amfani da mafarauta zai kawo karshen garkuwa da mutane a Nigeria - Sarki Sanusi

Yadda aka keta mana haddi a zaben 2019 - Yan takara mata
Yadda aka keta mana haddi a zaben 2019 - Yan takara mata
Asali: Twitter

Haka zalika, Mrs. Christina Ude, wacce ta tsaya takarar kujerar majalisar tarayya a mazabar Orlu/Oru ta Gabas da kuma Orsu, a jihar Imo, ta ce ta fuskanci jerin barazana kwanakin kadan kafin zabe.

"Wani ya kirani a waya yana yi mun barazana da cewar zai aiko 'yan ta'adda domin ganin ba a zabeni ba ma damar ban bashi wasu kudade ba. Kuma dai mutumin sai da ya aiwatar da kudurinsa domin ya aiko da 'yan ta'adda inda suka ci zarafin wakilai na, wasu lokutan ma har korarsu sukai," a cewar Ude.

Ta ce jama'a sun samu shuwagabannin da suka dace da su don haka bai kyautu a nan gaba su yi korafin samun mumman shugabanci ba, saboda sun zabesu ne bayan da aka basu kudi a rumfar zabe.

A nata bangaren, Mrs. Phina Kanu wacce ta yi takara a majalisar dokokin jihar Abia karkashin jam'iyyar APC ta ce anci zarafinta a yayin da ta je kad'a kuri'arta.

A cewarta, babu sauki a siyasar mace a wannan zamani, tana mai cewa ta fuskanci kalubale mai muni a yayin zaben 2019, ta yadda har sai da magoya bayanta suka tsere domin tsira da rayukansu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel