Amfani da mafarauta zai kawo karshen garkuwa da mutane a Nigeria - Sarki Sanusi

Amfani da mafarauta zai kawo karshen garkuwa da mutane a Nigeria - Sarki Sanusi

- Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya shawarci gwamnat da ta yi amfani da mafarauta domin magance matsalar garkuwa da mutane a Arewacin Nigeria

- Sanusi ya ce a ita ma jihar Kano ta Kudu ta fuskanci irin wannan matsalar shekaru hudu da suka gabata, amma da suka yi amfani da mafarauta an samu nasara

- Sarkin ya shawarci gwamnatin tarayya da ta yi amfani da tawagar mafarauta, sojoji, 'yan sanda, civil defence domin kawo karshen garkuwa da mutane a Zamfara da Kaduna

Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya shawarci gwamnatin tarayya da ta yi amfani da mafarauta domin magance matsalar garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta'addanci da ke ci gaba da mamaye shiyyar Arewacin Nigeria.

Sarki Sanusi, wanda ya bada wannan shawarar a yayin wani taro na shuwagabannin mafarauta a Kano a ranar Lahadi karkashin kungiyar masu kishin ci gaban jihar Kano (KCCI), ya ce jihar Kano ta gwada irin hakan, kuma an samu nasara.

Da ya samu wakilcin hakimin Doguwa, Dan Amar na Kano, Alhaji Aliyu Harazimi, Sanusi ya ce a cikin shekaru hudun da suka gabata, Kano ta Kudu ta kasance cikin fargaba saboda yawaitar garkuwa da mutane da kuma fashi da makami.

KARANTA WANNAN: Kiwon lafiya: Dalilin da zai sa mata su daina sanya matsattsun wandunan roba - Dr Mbume

Amfani da mafarauta zai kawo karshen garkuwa da mutane a Nigeria - Sarki Sanusi
Amfani da mafarauta zai kawo karshen garkuwa da mutane a Nigeria - Sarki Sanusi
Source: UGC

Ya ce: "A lokacin da garkuwa da mutane ya tsananta a dajin Falgore da ke karamar hukumar Doguwa, mun gayyaci mafarauta kuma muka samar da watatawagar tsaro ta musamman da suka hada da sojoji, 'yan sanda, civil defence da maharba.

"Mun samu nasarar lalata sansanonin masu garkuwa da mutane guda shida da ke a cikin dajin. A yanzu dai shekaru hudu ke nan tunda jami'an suka kai wannan sumame, har yanzu bamu sake jin an yi garkuwa da wani a dajin ba."

Sarki Sanusi ya baiwa gwamnatin tarayya shawara kan cewar ya kamata ta samar da makamanciyar wannan tawagar domin kawo karshen garkuwa da mutane a jihohin Zamfara Kaduna da sauran jihohin da lamarin ya shafa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel