Ado Doguwa, Kawu Sumail, da sauran zababbun yan majalisar Kano 22 sun bayynaa goyon bayansu wa Femi Gbajabiamila

Ado Doguwa, Kawu Sumail, da sauran zababbun yan majalisar Kano 22 sun bayynaa goyon bayansu wa Femi Gbajabiamila

Dukkan zababbun yan majalisar wakilan tarayya 24 daga jihar Kano sun yi alkawarin goyon bayan Mista Femi Gbajabiamila a matsayin sabon kakakin majalisar wakilan tarayya na tara .

Sun yanke wannan shawara a ganawarsu da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a ranar Asabar, 6 ga watan Afrilu, 2019 a birnin tarayya Abuja.

Mai magana da yawun yan majalisan kuma bulaliyar majalisa, Alhassan Ado Doguwa, ya ce wannan sharawa da suka yanke sun yi ne domin biyayya ga kwamitin gudanarwan jam'iyyar APC wacce ta ce a baiwa yankin kudu maso yamma kujerar kakaki.

Doguwa wanda ya samu nasara a zaben kujerar majalisar wakiai mai wakiltan Tudun Wada/Doguwa ya kara da cewa:

"Dukkanmu 24 mun tattauna, kuma mun yi ittifakin cewa a matsayinmu na wakilan al'ummarmu, za mu goyawa Femi Gbajabiamila bayan a matsayin kakakin majalisar wakilai karkashin jagorancin gwamnanmu, Dakta Ganduje, da shugaban jam'iyyarmu na jiha."

Kakakin majalisar dokokin jihar Kano kuma zababben dan majalisan wakilai mai wakiltar Rano/Kibiya/Bunkure, Kabiru Alhasan Rurum, ya kara jaddada wannan matsaya tasu.

Gwamna Abdullahi Ganduje a jawabinda ya godewa zababbun yan majalisan bisa ga biyayyar da suka yiwa shugabancin jam'iyyar.

Akwai kishin-kishin cewa yan majalisar Kano suna goyon bayan Gbajabiamila ne saboda su samu kujerar mataimakin kakakin majalisa kuma su baiwa Hanarabul Kawu Sumaila.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel