Za mu fara kama matan Fulani masu shigowa birni idan mazajensu basu daina kai hare-hare ba - Gwamnatin jihar Zamfara

Za mu fara kama matan Fulani masu shigowa birni idan mazajensu basu daina kai hare-hare ba - Gwamnatin jihar Zamfara

A ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu, Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa yan kabilar Fulani ne ke kai hare-hare sassan jihar da ya hallaka daruruwan mazauna a jihar.

Kwamishanan kananan hukumomi da masarautun gargajiya, Bello Dankande Gamji, ya bayyana hakan ne a ganawa da yayi tare da jami'an tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin Fulani da shugabannin kananan hukumomi a Gusau, babbar birnin jihar.

Game da cewarsa, rahotannin leken asiri sun nuna cewa yan Fulani zalla ke kai wadannan hare-hare a fadin jihar.

Ya umurci shugabannin Fulani su gana da wadannan yan bindiga domin shawo kan al'amarin saboda ba zai yiwu wasu yan tsiraru su hana sauran al'umma zaman lafiya ba.

Bello Dankande ya yi gargadin cewa idan har wannan hare-hare bai daina ba, gwamnatin jihar za ta damke dukkan matan Fulanin da ke shigowa birni sayar da Fura da Nono a jihar.

KU KARANTA: Tirkashi: Mahaukaci ya hallaka dan sanda har lahira

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa za ta dauki matsafa 1,700 domin taimakawa jami'an Civilian Joint Task Force (CJTF) 8,500 da aka dauka a baya domin kawar da al'amarin rashin tsaron da jihar ke fuskanta.

Kwamishanan kananan hukumomi da masarautun grgajiya, Alhaji Bello Dankande, ya laburta hakan ne a Gusau ranar Laraba, a ganawar samar da tsaro tare da sarakunan gargajiya, shugabannin Fulani, da shugabannin kananan hukumomin jihar.

A shekarar 2018, gwamnan jihar ya dauki yan kungiyar CJTF 8,500 domin kawo karshen al'amarin tsaron da ya addabi jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel