Yadda Nyesom Wike ya lashe zaben Gwamnan jihar Ribas

Yadda Nyesom Wike ya lashe zaben Gwamnan jihar Ribas

Dan takarar kujerar gwamnan jihar Ribas a karkashin ta jam'iyyar PDP, Nyesom Wike, a ranar Larabar da ta gabata hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta tabbatar da nasarar sa a matsayin wanda ya lasaben zaben da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris.

Gwamna Wike ya yi nasara a kananan hukumomi 19 cikin 21 da jihar Ribas ta kunsa, inda hukumar INEC ta kaddamar da cewa ya lashe zaben da kimanin kuri'u 88,264 yayin da ya lallasa babban abokin adawar sa na jam'iyyar AAC, Biokpomabo Awara, wanda ya samu kuri'u 173,857 kacal.

Yadda Nyesom Wike ya lashe zaben Gwamnan jihar Ribas
Yadda Nyesom Wike ya lashe zaben Gwamnan jihar Ribas
Asali: Depositphotos

Babban Baturen zabe na jihar da ya kasance Mataimakin shugaban jami'ar tarayya ta Otueke da ke jihar Bayelsa, Farfesa Teddy Adias, shi ne ya fayyace sakamakon zaben da ya tabbatar da nasarar dan takara na jam'iyyar PDP.

Gwamna Wike ya yi nasara a kananan hukumomin 19 da suka hadar da Port Harcourt, Ikwere, Andoni, Eleme, Opobo -Nkoro, Bonny, Okirika, Omuma, Tai, Ahoada East, Emuoha, Etche, Ogba/Egbema/Ndoni, Obio-Akpor, Asari-Toru, Ogu/Bolo, Ahoada west, Khana da kuma Degema.

KARANTA KUMA: Zaben Ribas: Atiku ya taya Gwamna Wike murnar samun nasara

Kasancewar ta al'ada yayin kowane zabe, dole a samu wanda ya yi nasara da kuma kishiyar hakan, duk da shan kaye Mista Awara dan takara na jam'iyyar AAC ya yi nasara a kananan hukumomin Akuku-Toru da kuma Oyibo.

Shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Ogbuah, yayin taya Gwamna Wike murnar samun nasara, ya ce nasarar ba ta takaita kadai a kansa illa iyaka ta hadar da dukkanin al'ummar jihar Ribasa masoya dimokuradiyya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel