Allah ya tsare: Yadda aka yi garkuwa da wasu masu kasuwancin gawayi a Kaduna

Allah ya tsare: Yadda aka yi garkuwa da wasu masu kasuwancin gawayi a Kaduna

- Wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne sun sace wasu masu kasuwancin itace guda 12 a kauyen Daga-fada da ke karamar hukumar Birnin Gwari, jihar Kaduna

- An samu rahoton cewa mutanen sun shiga dajin ne domin yankan itace, sana'ar da suka dauke ta hanyar daukar dawainiyar rayuwarsu da ta iyalansu a garin

- Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda na jihar, Yakubu Sabo, bai daga wayarsa ba har zuwa lokacin tattara wannan rahoto

Wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne sun sace wasu masu kasuwancin itace guda 12 a kauyen Daga-fada da ke karamar hukumar Birnin Gwari, jihar Kaduna. Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 7 na safiyar ranar Talata a kauyen da ke kusa da iyakar jihohin Kasduna da Niger.

An samu rahoton cewa mutanen sun shiga dajin ne domin yankan itace, sana'ar da suka dauke ta hanyar ci, sha, da kuma daukar dawainiyar rayuwarsu da ta iyalansu a garin.

Wani mazaunin Birnin Gwari wanda kuma yana daya daga cikin mambobin hadin guiwar jami'an tsaron sa kai (JTF) a garin ya shaidawa manema labarai cewa mafi yawancin wadanda aka sace mazauna garin Birnin Gwari ne.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Shugaba Bouteflika na Algeria zai yi murabus kafin ranar 28 ga Afrelu

Allah ya tsare: Yadda aka yi garkuwa da wasu masu kasuwancin gawayi a Kaduna
Allah ya tsare: Yadda aka yi garkuwa da wasu masu kasuwancin gawayi a Kaduna
Asali: Facebook

Ya ce har yanzu dai wadanda suka yi garkuwa da su ba su tuntubi iyalansu ba.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda na jihar, Yakubu Sabo, bai daga wayarsa ba har zuwa lokacin tattara wannan rahoto.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel