Daukar ma’aikata na 2019: Rundunar sojin ruwa ta bayyana ranar jarabawa

Daukar ma’aikata na 2019: Rundunar sojin ruwa ta bayyana ranar jarabawa

Rundunan sojin ruwa ta bayyana cewa zata gudanar da jarabawan daukar ma’aikata na shekarar 2019 a ranar 13 ga watan Afrilu a cibiyoyi 30 dake fadin kasar nan.

Kakakin rundunan sojin ruwa, Commodore Suleman Dahun ne ya bayyana haka a wani jawabi da yayi a Abuja.

Ya bayyana cewa: “Rundunan Sojin ruwa na burin sanar da al’umma cewa zata gudanar da jarabawar gwaji na daukar ma’aikata na shekarar 2019, za a gudanar da shirin ne a ranar 13 ga watan Afrilu a cibiyoyi 30 da ke fadin kasar.

Daukar ma’aikata na 2019: Rundunar sojin ruwa ta bayyana ranar jarabawa
Daukar ma’aikata na 2019: Rundunar sojin ruwa ta bayyana ranar jarabawa
Asali: UGC

“Ana sa ran masu neman aikin zasu bayyana da karfe 8:00 na safe a cibiyoyin da sunayen su ya fada yayin da suka yi rijista a yanar gizo.”

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Shugaba Bouteflika na Algeria zai yi murabus kafin ranar 28 ga Afrelu

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Makarantar horas da sojoji ta Kaduna (NDA) ta sanar da cewa ta dakatar da zana jarabawar shiga makarantar, ga daliban zango na 71. Abubakar Abdullahi, jami'in hulda da jama'a na NDA, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Litinin a Kaduna.

A cewar sa, yanzu an dakatar da jarabawar wacce aka shirya zanawa a ranar 13 ga watan Afrelu. Abdullahi ya ce za a sanar da sabuwar ranar da za a sake gudanar da jarabawar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel