Dalilin dakatar da zana jarabawar shiga makarantar horas da sojoji ta Kaduna - NDA

Dalilin dakatar da zana jarabawar shiga makarantar horas da sojoji ta Kaduna - NDA

- Makarantar horas da sojoji ta Kaduna (NDA) ta sanar da cewa ta dakatar da zana jarabawar shiga makarantar, ga daliban zango na 71

- NDA ta ce za a sanar da sabuwar ranar da za a sake gudanar da jarabawar

Makarantar horas da sojoji ta Kaduna (NDA) ta sanar da cewa ta dakatar da zana jarabawar shiga makarantar, ga daliban zango na 71. Abubakar Abdullahi, jami'in hulda da jama'a na NDA, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Litinin a Kaduna.

A cewar sa, yanzu an dakatar da jarabawar wacce aka shirya zanawa a ranar 13 ga watan Afrelu. Abdullahi ya ce za a sanar da sabuwar ranar da za a sake gudanar da jarabawar.

KARANTA WANNAN: Takardar cin zabe: INEC ba ta so na zama shugaban majalisar dattijai - Uwajumogu

"NDA na son sanar da dukkanin wadanda suka cike b ukatar shiga makarantar a zango na 71 cewa jarabawar shiga makarantar da aka shirya gudanarwa a ranar 13 ga watan Afrelu 2019 an dakatar da ita," cewar kakakin NDA.

"Zamu sanar da jama'a sabuwar ranar da za a zana jarabawar."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel