Inna lillahi wa inna ilayhi raji'un: Manoma 10 sun mutu a sabon harin Zamfara

Inna lillahi wa inna ilayhi raji'un: Manoma 10 sun mutu a sabon harin Zamfara

- Wasu 'yan bindiga sun kashe manoman albasa g10 a kauyen Kursasa da ke gundumar Kware, karamar hukumar Shinkafi, jihar Zamfara

- Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda na jihar, SP Muhammad Shehu ya tabbatar da kai harin amma ya ce tuni aka tura jami'an tsaro garin

- Tsakanin watan Fabreru zuwa Maris, akalla mutane 62 ne aka kashe a wasu manyan hare hare guda biyu da aka kai gundumar

Rahotannin da muka samu na nuni da cewa wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne sun kashe wasu manoman albasa guda 10 a kauyen Kursasa da ke gundumar Kware, karamar hukumar Shinkafi, jihar Zamfara.

Gundumar Kware dai ta dade tana fuskantar hare haren ta'addanci a cikin makonni shida. Tsakanin watan Fabreru zuwa Maris, akalla mutane 62 ne aka kashe a wasu manyan hare hare guda biyu da aka kai gundumar.

KARANTA WANNAN: Da zafinsa: Gbajabiamila ne ya fi cancanta ya zama kakakin majalisar wakilai - Abdulmumin Jibrin

Mazauna garin Kursasa sun shaidawa Daily Trust cewa 'yan bindigar sun shiga garin haye aan babura inda suka budewa manoman wuta da ke aiki a gonakinsu na albasa. Manoma sun yi iya bakin kokarinsu na tsira da rayuwarsu amma 'yan bindigar suka fi karfinsu.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda na jihar, SP Muhammad Shehu ya tabbatar da kai harin amma ya ce tuni an tura jami'an tsaro garin domin kwantar da hankulan jama'a da kuma tabbatr da tsaro.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel