Tarihin Umaru Fintiri da ya doke Gwamnan APC a zaben 2019
Kwanan nan ne Alhaji Ahmadu Umaru Fintiri ya samu nasara a zaben gwamnan jihar Adamawa. Umaru Fintiri na jam’iyyar PDP mai hamayya ya doke Gwamna mai-ci Mohammed Jibrilla Bindow na jam’iyyar APC mai mulki.
Mun kawo maku kadan daga cikin tarihin rayuwa da siyasar gwamnan na jihar Adamawa mai jiran-gado.
1. Haihuwa
An haifi Umar Fintiri ne a cikin Watan Oktoban shekarar 1967. Hakan na nufin Fintiri zai hau gwamna yana da shekaru 51 rak a Duniya. An haifi Fintiri ne a cikin Garin Madagali da ke cikin jihar ta Adamawa.
2. Karatu
Umaru Fintiri ya soma karatu ne a babbar makarantar Firamare da ke cikin Garin Gulak a 1975. Bayan ya kammala ya zarce har Sakandare tsakanin 1981 zuwa 1986. Fintiri yayi Digiri ne a jami’ar Maiduguri.
KU KARANTA: Abubuwa 5 da ya kamata ka sani game da Asiwaju Bola Tinubu
Sabon gwamnan ya kammala Digirin sa a fannin tarihi ne a cikin shekarar 1992. Bayan nan kuma daga baya ya koma jami’ar tarayyar da ke jihar Borno domin samun karin shaidar karatu a 2004. Fintiri yayi wa kasa hidima a shekarar 1993.
3. Siyasar Majalisa
Fintiri ya rike mukamin shugaban marasa rinjaye a majalisar dokoki tun daga 2007 har 2011. A 2011 ne ya zama mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Adamawa, wanda daga baya kuma ya rike matsayin shugaban masu rinjaye.
A tsakiyar 2014 ne aka nada Rt. Hon. Umaru Fintiri a matsayin kakakin majalisar dokoki na jihar Adamawa. Hakan ya kai sa ga rike mukamin gwamna na rikon kwarya a jihar bayan majalisar sa ta tsige gwamna Murtala Nyako a 2014.
4. Neman Gwamna a PDP
A bara ne kuma Ahmadu Umaru Fintiri ya nemi tikitin gwamna a APC inda ya zo na daya. Fintiri ya doke wani babban Hadimin Goodluck Jonathan watau Ahmad Waziri, da tsohon mataimakin gwamnan Adamawa Bala James Ngillari.
Ahmadu Umaru Fintiri ya kuma tika ‘yan siyasa irin su Aliyu Ahmed da Dr. Umar Ardo wajen samun tuta a karkashin jam’iyyar PDP mai adawa a jihar. Fintiri ya samu kuri’a sama da 1, 600 a zaben.
5. Takarar Gwamna
Alhaji Umar Fintiri ya lashe zaben gwamnan Adamawa ne da aka yi bayan zaben ya kai ga zagayen cike-gibi da farko. Umar Fintiri ya tashi da kuri’a 376,552 inda ya doke gwamnan da ke kan mulki Jibrilla Bindow da kuri’u 336,386.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng