Manyan limamai da malaman addini sun ziyari shugaba Buhari (Hotuna)
Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin jiga-jigan malamai da limamai manyan masallatan Najeriya a ranar Juma'a, 29 ga watan Maris, 2019 a fadar shugaban kasa dake AsoVilla, birnin tarayya, Abuja.
Daga cikin malaman da suka ziyarci shugaban kasa sune babban Murshid na babban Masallacin birnin tarayya, Farfesa Galadanci; sakataren kungiyar Jama'atu Nasril Islam, Sheik Khalid; da babban malami Dakta Mansur Sokoto.
Sauran sune Sheik Yakubu Hassan Katsina Sautus Sunnah, mataimakin limamin masallacin tarayya, da minisyan birnin tarayya, Muhammadu Bello.
KU KARANTA: An gudanar da Sallar Jana'izar dan majalisar wakilai, Muhammad Dantani Yellow
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng