Najeriya ce kasa ta 6 cikin jerin kasashen duniya mafi tabarbarewar tattalin arziki

Najeriya ce kasa ta 6 cikin jerin kasashen duniya mafi tabarbarewar tattalin arziki

Wani masanin tattalin arziki na jami'ar John Hopkins ta Baltimore a kasar Amurka, Steve Hanke, ya sanya Najeriya a mataki na shida cikin jerin kasashen duniya mafi girman tabarbarewa ta fuskar munin tattalin arziki.

Najeriya ce kasa ta 6 cikin jerin kasashen duniya mafi tabarbarewar tattalin arziki
Najeriya ce kasa ta 6 cikin jerin kasashen duniya mafi tabarbarewar tattalin arziki
Asali: UGC

Mista Hanke ya wallafa wannan kididdiga cikin mujallar Forbes a ranar 28 ga watan Maris, bayan gudanar da bincike da nazari akan yadda tattalin arzikin kasashen duniya ta fuskar rashin aikin yi, farashin riba yayin karbar bashi da sauran harkokin mu'amala da kudi.

Kwararren Malamin na jami'ar Baltimore tare da abokin tarayyar sa na nazari, Robert Barro na jami'ar Havard suka bayyana yadda tattalin arzikin kasar Najeriya ya dukurkushe musamman a sakamakon yadda rashin aikin yi ya tsananta.

KARANTA KUMA: Luwadi: Babban Fasto ya gogawa Saurayi cutar Kanjamau a jihar Legas

Cikin kididdigar da Mista Hanke ya fitar, ya sanya kasar Thailand da kuma Hungary a mataki na 94 da kuma 95 cikin jerin kasahen duniya mafi munin tattalin arziki. Hakan ya tabbatar da kasahen biyu a matsayin kasashe da suka kere sauran ta fuskar kyawun tattalin arziki.

Shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, sauran kasashen duniya biyar da suka shige gaban Najeriya ta fuskar durkushewar tattalin arziki sun hadar da Venezuela, Argentina, Iran, Brazil da kuma Turkey.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel