Shugabannin CUPP 50 sun ziyarci Ganduje domin taya sa murnar cin zabe (hotuna)

Shugabannin CUPP 50 sun ziyarci Ganduje domin taya sa murnar cin zabe (hotuna)

Rahotanni sun kawo cewa shugabannin hadakar jam’iyyun adawa ta ‘Coalition of United Political Parties’ (CUPP), sun ziyarci gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje a yau Laraba, 27 ga watan Maris.

Shugabannin kungiyar kimanin su 50 sun kai ziyarar ne domin taya gwamnan na jihar Kano murnar nasarar da yayi a zaben jihar a karo na biyu.

Shugaban kungiyar, Nuhu Isa Dan Fulani ne ya jagorance su zuwa gidan gwamnan.

Kakakin gwamnan na jihar Kano, Salihu Tanko Yakasai ne ya wallafa batun ziyarar a shafinsa na Facebook.

Shugabannin CUPP 50 sun ziyarci Ganduje domin taya sa murnar cin zabe (hotuna)
Shugabannin CUPP 50 sun ziyarci Ganduje domin taya sa murnar cin zabe
Asali: Facebook

Shugabannin CUPP 50 sun ziyarci Ganduje domin taya sa murnar cin zabe (hotuna)
Shugaban kungiyar, Nuhu Isa Dan Fulani ne ya jagorance su zuwa gidan gwamnan
Asali: Facebook

Shugabannin CUPP 50 sun ziyarci Ganduje domin taya sa murnar cin zabe (hotuna)
Shugabannin CUPP sun ziyarci Ganduje domin taya sa murnar cin zabe
Asali: Facebook

A halin da ake ciki, a baya Legit.ng ta rahoto cewa Jam'iyyar CUPP reshen Jihar Kano za ta kalubalanci nasarar da gwaman Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya samu a zaben ciki gibi na gwamna da aka gudanar a ranar Asabar 23 ga watan Maris.

KU KARANTA KUMA: Dattaku: Ganduje ya bayar da umurnin a mayar da hotunan Sarki Sanusi II a gidan gwamnati

Shugaban CUPP na jihar, Alhaji Muhammad Abdullahi Raji ne ya bayyana hakan yayin da ya ke zantawa da manema labarai a kan sakamakon zaben karo na biyu da aka gudanar inda Ganduje na jam'iyyar APC ya lashe zaben.

Daily Trust ta ruwaito cewa Raji ya ce Hadakar jam'iyyun da ta kunshi jam'iyyun siyasa 42 sun kammala shirye-shirye domin zuwa kotu domin kallubalantar sakamakon zaben.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel