Yanzu-yanzu: Alkalin kotun koli ya zama sabon sarkin Lafiyan Bare-bari

Yanzu-yanzu: Alkalin kotun koli ya zama sabon sarkin Lafiyan Bare-bari

Wani alkalin kotun kolin Najeriya, Sidi Dauda Bage, ya zama sabon sarkin masarautar Lafiya a jihar Nasawara.

Sabon sarkin na cikin Yarimomi 22 na masaurautar Lafiya da suka nemi kujerar saurautar wacce itace daya daga cikin mafi girma a masarautun gargajyan Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta samu rahoton cewa sabonnn Sarkin ya doke Yarimomi 15 daga gidansu wadanda suka tsaya takarar mulkin.

Sune, Alhaji Isiaka Dauda, Abdullahi Yusuf Musa II, Muhammadu Makama, Maisallau Musa II, Dunama Abubakar Ahmed, Mohammed Waziri Hamza, Mustapah Yahuza, Safiyanu Bage, Abdullahi Bage, Aliyu Muhammad Abdullahi, Abbas Ramalan Musa, Idris Yusuf Musa, Suleiman Muhammad Moyi Dan Nana, Muhammad Yusuf Jaje da Abdullahi Musa.

Kana ya doke wasu Yarimomin hudu daga gidan saurautar Laminu wadanda sune: Abdullahi Shuaibu Gayam, Muhammad Sarki, Ahmed Yahuza Laminu and Muhammad Saeed Laminu.

Hakazalika daga gidan sarautar Ari Dunama, Sarki Sidi Dauda Bage, ya doke Musa Isa Musthapaha Agwai da Abdullahi Aliyu Agwai.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai rage albashin wasu ma'aikata a kasar nan

A baya mun kawo muku rahoton cewa an gudanar da jana'izar sarkin Lafiya, Marigayi Isa AlMustapha Agwai I, cikin fadarsa ta garin Lafiya da ke jihar Nasarawa yayin da hawaye suka kwaranya tare da jimamin wannan babban rashi na kasar Najeriya baki daya.

An gudanar da jana'izar Sarkin garin Lafiya na 16 cikin fadarsa da ya riga mu gidan gaskiya a jiya Alhamis bayan wata 'yar gajeruwar rashin lafiya da ta zamto ma sa sanadiyar ajali.

Babban Limamin garin Lafiya, Malam Dalhatu Muhammad Dahiru, shine ya jagoranci sallar jana'izar da misalin karfe 3:15 na yammacin yau Juma'a tare da 'yan uwa, makusanta da abokanan arziki.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel