Yanzu Yanzu: Kotu ta soke zaben fidda gwani na APC a Zamfara

Yanzu Yanzu: Kotu ta soke zaben fidda gwani na APC a Zamfara

- Kotun daukaka kara da ke zaune a Sokoto ta jingine hukuncin wata babbar kotun Zamfara akan zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC)

- Lamarin ya shafi dan takarar jam'iyyar na gwamna, da na majalisun dokokin jiha da kasa

Kotun daukaka kara da ke zaune a Sokoto, karkashin jagorancin Justis Tom Yakubu, ya jingine hukuncin wata babbar kotun Zamfara akan zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Lamarin ya shafi samar da dan takarar gwamna da kuma yan takarar majalisun dokoki na jiha da kasa, NAN ta ruwaito.

Yanzu Yanzu: Kotu ta soke zaben fidda gwani na APC a Zamfara
Yanzu Yanzu: Kotu ta soke zaben fidda gwani na APC a Zamfara
Asali: UGC

Legit.ng za ta kawo Karin bayani da zaran ya bayyana.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Sanata mai wakiltan Zamfara ta Tsakiya, Kabiru Marafa ya sake jadada cewa bai dace a bari jam'iyyarsa ta APC ta tsayar da 'yan takara ba a zaben da za a gudanar a watan Fabrairu da Maris na wannan shekarar.

KU KARANTA KUMA: Sake zaben Gwamna: Hukumar INEC na karfafa ta’addanci - Tsohon kwamishinan Kano

Marafa ya ce Hukumar Zabe mai zaman kanta tayi biyaya da umurnin babban kotun Abuja inda ta yanke hukuncin cewa jam'iyyar ta APC ba za ta fitar da 'yan takara ba.

Sanatan wanda kuma shine Ciyaman din kwamitin majalisar dattawa a kan albarkatun man fetur ya yi wannan furucin ne yayin hirar da ya yi da menema labarai a babban birnin tarayya, Abuja. Ya ce INEC ta tsaya a kan bakar ta na haramtawa jam'iyyar APC reshen Zamfara fitar da 'yan takara saboda gaza gudanar da zaben fidda gwani a cikin lokacin da aka kayyade mata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel