Tamu ta samu: 'Yar arewa, ministar Buhari ta samu mukami na kasa-da-kasa a tarayyar Afrika

Tamu ta samu: 'Yar arewa, ministar Buhari ta samu mukami na kasa-da-kasa a tarayyar Afrika

Kungiyar tarayyar Afrika watau Africa Union (AU) a ranar Alhamis a garin Addis Ababa na kasar Itofiya ta nada ministar kudi ta tarayyar Najeriya, Zainab Shamsuna Ahmed a matsayin shugabar kwamitin amintatu na gidauniyar samar da zaman lafiya na kungiyar.

Kwamitin na amintattu kamar yadda muka samu yana da mambobi biyar ne kowane yana wakiltar yanki a Najiyar ta Afrika.

Tamu ta samu: 'Yar arewa, ministar Buhari ta samu mukami na kasa-da-kasa a tarayyar Afrika
Tamu ta samu: 'Yar arewa, ministar Buhari ta samu mukami na kasa-da-kasa a tarayyar Afrika
Asali: Twitter

KU KARANTA: Farashin Naira ya fadi warwas a kasuwannin hada-hada

A wannan tsarin, kamar yadda muka samu ita ministar ta shugaba Buhari tana wakiltar yankin Afrika ta yamma ne idan aka hada da shugabancin kwamitin.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawun ta, Mista Paul Ella Abechi ya fitar dauke da sa hannun sa inda kuma ya godewa kwamitin da ya ga cancantar nada ta shugabance su.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa Zainab Shamsuna a da ita ce karamar minista a ma'aikatar kudi ta gwamnatin shugaba Buhari kafin daga bisani Ministar ma'aikatar Femi Adeosun ta yi murabus a shekarar da ta gabata.

A wani labarin kuma, Sabbin alkaluman kiwon lafiya na duniya sun nuna cewa kasar Najeriya a yanzu ita ce ta farko a jerin kasashen da suke fama da cutar kyanda inda alkaluma suka nuna cewa akalla yara a kasar sama da miliyan uku ne ba a yi masu rigakafin cutar ba a halin yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel