Lafiya jari: Najeriya ta zo na daya jerin kasashen duniya dake fama da cutar kyada

Lafiya jari: Najeriya ta zo na daya jerin kasashen duniya dake fama da cutar kyada

Sabbin alkaluman kiwon lafiya na duniya sun nuna cewa kasar Najeriya a yanzu ita ce ta farko a jerin kasashen da suke fama da cutar kyanda inda alkaluma suka nuna cewa akalla yara a kasar sama da miliyan uku ne ba a yi masu rigakafin cutar ba a halin yanzu.

Shugaban dake kula da hukumar lafiya ta duniya watau World Health Organisation (WHO), a jihar Borno mai suna Dakta Audu Idawo shine ya bayya hakan a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar domin shirya tunkarar aikin rigakafin cutar.

Lafiya jai: Najeriya ta zo na daya jerin kasashen duniya dake fama da cutar kyada
Lafiya jai: Najeriya ta zo na daya jerin kasashen duniya dake fama da cutar kyada
Asali: UGC

KU KARANTA: Maimaita zabe: 'Yan sanda a Filato sun daura damarar ko-ta-kwana

Legit.ng Hausa dai ta samu cewa ayyukan riga-kafin dai za su gudana ne daga ranar 21 zuwa 25 ga watan Maris tare da hadin gwuiwar ma'aikatar lafiya ta tarayyar Najeriya da kuma tallafin gidauniyar lafiya ta kananan yara watau United Nations Children’s Fund (UNICEF).

A wani labarin kuma, Uwar gidan shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari ta shawarci 'yan Najeriya da su rika zuwa gwajin cutar nan ta tarin fuka akai akai domin sanin matsayi da kuma neman magani idan tsautsayi ya gitta.

Uwar gidan Shugaban kasar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar manema labarai da rarraba a ranar Laraba ta bayyana cewa alamomin cutar ta tarin fuka sun hada da yin tari ba kakkautawa har na tsawon sati biyu a jere.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel